Jam’iyyar APC reshen jihar Gombe ta nada kwamiti da za ta binciki zargin yi wa jam’iyyar da ɗan takarar ta a jihar Gombe yankan baya a zaɓen da ya gabata.
Shugaban jam’iyyar na gundumar Keshere, Tanimu Abdullahi, ya ce an kafa kwamitin ne bisa zargin da aka samu cewa sanata Danjuma Goje ya umarci magoya bayan sa da shi kansa su zaɓi wani ɗan takara da ba na APC ba.
” Dalilin gano cewa akwai makarkashiya da Goje ya kulla tare da magoya bayan sa na yi wa wani ɗan takara da ba na jam’iyyar APC ba aiki a zaben 2023, ya sa aka nada kwamiti domin a gudanar da bincike akan haka.
Abdullahi ya ce ba zai yiwu a zuba masa ido ya rika abinda ya ga dama bayan a ita jam’iyyar APC ɗin ne ya ke cin moriyar siyasar sa.
An ba kwamitin makonni biyu su muka rahoton aikin da suka yi.
Discussion about this post