Gwamnan jihar Zamfara Bello Matawalle ya bayyana cewa gwamnatin tarayya ne ta turo sojoji suka murde zaben gwamnan Zamfara domin PDP ta yi nasara.
Idan ba a manta ba Matawalle ya saha kayi a zaben gwamnan da aka gudanar ranar 18 ga Maris.
Dauda Lawal ya kada Matawalle da kuri’u sama da 60,000 a zaben.
Wannan kayi da matawalle ya sha ya yi matukar tada masa da hankali domin shigar bazata aka yi masa.
Sai dai kuma Matawalle ya yi zargin cewa da gangar aka shirya wannan tuggu na a kada shi a zaben gwamman, Ya ce daga Abuja aka turo zaratan sojoji zuwa jihar Zamfara domin su kada shi don ya kalubalanci sauya canjin takardun Naira da gwamnati ta yi.
Sojojin ba su boye kansu ba. Kurukuru suka fadi ko ka zabi PDP ko ka sha dukan tsiya. Da muka yi kira ga gwamnatin Tarayya ta kawo mana dauki a lokacin maganan tsaro ba a turo mana ba, amma da ya ke maganar siyasa ce kuma ba ason mu an kawo zaratan sojoji su tilasta wa mutane su zabi abin da ba shi suke so ba.
” Da ma an fadi mana cewa ba dai mun tafi kotu saboda canjin takardun kudi ba, zamu gani a kwaryar mu. Da ni da Nasir El-Rufai, da Ganduje na Kano, shine fa suka tabbatar sun kada ni da karfin tsiya.
A karshe matawalle ya ce zai bar wa jam’iyyar Ta APC ta dauki matsaya ko za ta tafi kotu ko kuma A’A.