Zababben gwamnan jihar Kaduna Uba Sani ya ce zai kalubalanci sakamakon zaben da jami’yyar adawa ta PDP ta yi nasara da su a wasu kanan hukumomin jihar.
Uba Sani ya nuna matukar mamakinsa kan yadda jami’yyar PDP ta wawushi kuri’u a wasu kananan hukumomi a zaben gwamnan jihar.
Ya ce zai garzaya kotun sauraron kararrakin zabe domin kalubalantar sakamakon da yake ganin idan aka yanke hukunci zai yi wa Ashiru nisan da bashi misaltuwa.
Idan ba a manta ba a ranar Litini ne baturen zabe Kuma Shugaban Jami’ar Usman Dan Fodio dake jihar Sokoto farfesa Lawal Bilbis ya bayyana Uba Sani wanda ya ci zaben gwamnan Kaduna.
Bisa ga sakamakon zaben da INEC ta bayyana Uba Sani ya samu kuri’u 730,002 Isa Ashiru na PDP ya samu kuri’u 719,196. Akwai ratar kuri’u 10,806 a tsakaninsu.
Sani wanda ya bayyana cewa an yi magudi a zaben musamman a wuraren da PDP ta yi nasara ya bada misalin karamar hukumar Chikun inda a nan jami’yyar PDP ta samu kuri’u 89,000 da ya ke ganin hakan ba gaskiya bane.
Bayan haka zababben gwamnan ya yi wa mutanen Kaduna alkawarin yin adalci ga kowa da kowa harda wadanda basu zabe shi ba.
Ya ce yana farin ciki da sakamakon zaben domin mutane sun fito sun zabe shi.