Rundunar ‘yan sandan Kaduna sun gargadi yan jihar da su shiga taitayin su kada wani ya ce zai fito yayi bikin nasara ko rashin nasara a zaben da aka kammala a karshen makon jiya.
Kakakin rundunar na jihar Kaduna Mohammed Jalige, a wata takarda da ya fitar ranar Laraba ya ce domin a samu zaman lafiya da dakile tada zaune tsaye da wasu ke kokarin yi, rundunar na gargadin mazauna jihar kada su fito yin biki ko taron murnar nasarar wani dan takara a jihar.
” Duk wanda ya ki ji ba ya ki gani ba. Ina so in tabbatar muku da kuma ja muku kunne cewa duk wanda ya nemi ya tada zaune tsaye a jihar Kaduna ta hanyar yin biki ko zanga-zanga, zai dandana kudar sa a wannan jiha. Lallai kowa fa ya tabbata ya dauki wannan abu da mahimmancin gaske domin ba za a kyale shi ba idan ya aikata laifi.
Idan ba a manta ba a sakamakon zabukan da aka bayyana a garin Kaduna Jam’iyyar APC mai mulki a jihar ta sha kashi a hannun mutanen jihar.
Jam’iyyar PDP ta lallasa APC a zaben kujerun majalisun jihar. Bi sa ga sakamakon zaben, PDP ta lashe kujeru 10 na majalisun tarayya, APC 4 sai kuma LP kujeru biyu.
haka kuma jam’iyyar ta rasa duka kujerun ta biyu na sanata wanda take akai a baya.