Ɗan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya kalubalanci sakamakon zaɓen shugaban kasa wacce hukumar zaɓe ta bayyana Bola Tinubu na APC a matsayin wanda ya lashe zaɓen.
Idan ba a manta ba tun bayan bayyana sakamakon zaɓen da hukunar zaɓe ta yi gaggan ƴan takarar Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na Labour Party suka yi watsi da sakamakon suka ce an tafka maguɗi a cikin sa.
Atiku ranar Laraba ta hanyar Lauyoyinnsu sun shigar da karar cewa basu yarda da sakamakon zaɓen.
A cikin takardar korafin da lauyoyin Atiku suka mika wa kotu, sun ce korafi na ɗaya shine, Lallai Atiku ya lashe zaɓe bisa ga dukkan bayanan da suka da shi, an murɗe mai su ne.
Sannan buƙata ta biyu itace idan mika masa shugabanci kai tsaye ba zai yiwu ba, to lallai a soke zaɓen kawai a sake zaɓen shugaban kasa tun daga farko.
Bayan haka Atiku ya ce idan kuma hakan ba zai yiwu ba kotu ta yanke hukuncin su biyun su gwabza wanda ya yi nasara a ba shi shugabancin Najeriya.
PREMIUM TIMES HAUSA ta bugabyadda Atiku ya yi fatali da gayyatar da Tinubu yayi masa na azo a haɗa hannu tare don ci gaban kasa.
Atiku, ya ce munaficci kawai da Tinubu ya ke ta ƙoƙarin jawo shi a jika ya na neman haɗin kan sa, bayan an yi zaɓe cikin hargitsi da rigingimu.
A cikin wata sanarwa da Tinubu ya fitar kuma ya sa mata hannu da kan sa, ya nuna rashin jin daɗin sa da ‘yan kura-kuran da su ka faru a wasu yankuna a lokacin gudanar da zaɓe.
Mataimakin Hadimin Yaɗa Labarai na Atiku, wato Phrank Shaibu, ya bayyana kiran da Tinubu ya cewa munaficci ne kawai.
Ya ce rashin kunya ce kawai za ta sa Tinubu ya nemi haɗin kai bayan kammala zaɓe, alhali magoya bayan sa sun riƙa kai wa ƙabilar Igbo hari a ranar zaɓe a Legas.
Ya ce har yanzu Tinubu bai daina goyon bayan ‘yan tasha a Legas masu wulaƙanta mutane a Legas.
Daga nan kuma Atiku ya yi kira a kama shugaban ‘yan tashar Legas, wanda ya ce ya na cikin Kwamitin Kamfen ɗin TInubu.
Discussion about this post