Shugaban Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), Farfesa Mahmood Yakubu ya ƙaryata zargin cewa ya yi wa zaɓen gwamnan Jihar Abiya Katsalandan.
Sakataren Yaɗa Labarai na Yakubu, Rotimi Oyekanmi ya ce labarai da bayanan da wasu ke yaɗawa duk ƙarairayi ne da kame-kame kawai.
Ya ce Yakubu bai wai ba babbar jami’ar zaɓen jihar umarnin aikatawa ko aiwatar da wani abu da ya kauce wa tsarin dokokin zaɓe ba dangane da tattara sakamakon zaɓen Abiya.
Ya ce ita Babbar Jami’ar Zaɓe ta jihar ce ta tambaye shi matakin da za ta ɗauka na gaba, dangane da batun tattara ƙuri’un zaɓen gwamnan jihar.
“Daga nan ne shi kuma Shugaban INEC ya umarce ta da ta tura wa Kwamishinan Zaɓe na Jihar Enugu sakamakon zaɓen da ce cikin kwanfuta, kafin a kai kwafe-kwafen na takardu. Ya ce a aika Kwamishinan Zaɓe na Enugu shi da Sakataren Gudanarwa na hukumar a Enugu.
Daga nan ya nuna rashin jin daɗin “yadda wasu mutane da gangan su ka riƙa shirya ƙarairayi su na cewa “wai Shugaban INEC ya bai wa Babbar Jami’ar Zaɓe ta Abiya umarnin da ya kauce wa dokokin INEC. Amma a gaskiya ba haka ba ne, zargin ba gaskiya ba ne.”
Daga nan Oyekanmi ya ja hankalin jama’a su guji irin wannan labari na maƙaryata ne su ka kitsa shi, kuma labarin bogi ne.
A ranar Talata ce dai wata manhajar ‘Strenuous Blog’ ta ruwaito Jami’ar Zaɓen Jihar Abiya ta ce Shugaban INEC ya kira ta a wayar ta, ya yi ƙoƙarin ba ta umarnin da ba ya kauce wa dokokin zaɓe. Rahoton ya ce matar ta yi iƙirarin cewa idan ta bi umarnin sa, to abin da za ta aikata zai shafi sakamakon da al’ummar Abiya su ka zaɓa.
“Ita ce da kan ta nemi matsayar INEC dangane da dakatar da tattara sakamakon zaɓen Jihar Abiya.
“Daga nan ne sai Shugaban INEC ya ce mata ta tura kwafen wasiƙar sakamakon ga Kwamishinan Zaɓe na Enugu, kafin a kai kwafen takardun sakamakon.”
Oyekanmi ya ce Hukumar Zaɓe ko shugaban ta ba su wani nuƙu-nuƙun bada umarnin da ya kauce wa dokar INEC,” Inji Oyekanmi.
Discussion about this post