Sakamakon Zaɓe da ke ci gaba da fitowa a jihohin faɗin kasar nan na nuna cewa a wasu jihohin an samun yadda ake so wasu kuma jam’iyyu na kokawa wasu kuma suna shan kasa.
A jihar Kaduna, Sakamakon karamar hukumar Zariya wanda baturen zaɓe ya bayyana ya nuna jam’iyyar APC ce ta lashe karamar hukumar inda ta baiwa Isah Ashiru na PDP ratar kusan kuri’u 30,000.
A sakamakon da aka bayyana zuwa, APC, wato Uba Sani ya samu Kuri’u 78, 659 shi kuma Isah Ashiru ya samu kuri’u 47,091.
An kammala faɗin sakamakon zaɓen Zaria sannan tuni har an nausa da su Kaduna domin bayyana wa.
Discussion about this post