Fitaccen mai yin sharhi akan siyasar Najeriya, Bulama Bukarti ya bayyana cewa korafin da wasu ƴan takara ke yi cewa wai don ba a saka sakamakon zaɓe a rumbun iRev ba, shikenan zaɓen bai inganta ba, cewa ba haka bane.
A tattaunawa da ya yi da BBC Hausa Bukarti ya ce ” A iya fahimta ta, babu wanda zai iya rushe wannan zaɓe saboda wai kawai ba a saka sakamakon zaɓen a manhajar (rumbun) iRev ba a yanar gizo.
” A ƙa’idar dokar zaɓe ba sai lallai irin wannan ne ya ke sa a soke zaɓe ba sai an samu mummunar rashin bin dokar zaɓen. Sannan kuma sai abin ya kai matsayin da ya canja sakamakon zaɓen wanda babu wanda cikin su ko korafi akai.
” Sannan kuma a sani na shugaban hukumar zaɓe ba shi da ikon yace ya rushe wannan zaɓe baki ɗaya. Haka kuma shima shugaban kasa da Obasanjo ya rubuta wa wasika bashi da ikon rushe wannan zaɓe baki daya.
” Yanzu so suke a rushe wannan zaɓe sannan a sake komawa a ware wasu naira biliyan 40 domin zaɓen. Abinda nake ganin ya fi dacewa shine waɗanda ke da ƙorafi su tatara korafe korafensu su garzaya kotu.
” Amma a ganina babu kotu a wannan duniya da zata soke wannan zaɓe.
Idan ba a manta ba manyan jam’iyyun adawa sun yi korafin cewa wai don ba a saka sakamakon zaɓe a manhajar rumbun iRev ba shikenan a soke zaɓen a sake wata.
Jam’iyyar PDP da na LP sune kan gaba wajen kira da a soke zaben a sake wata. Haka shima tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya yi wasika ga shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya soke zaɓen a sake wata.