Kusan Asubahin ranar Laraba ce INEC ta bayyana Bola Tinubu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
Shugaban Hukumar Zaɓe (INEC) ta Ƙasa, Farfesa Mahmood Yakubu ya bayyana Bola Tinubu, ɗan takarar shugaban ƙasa na APC a matsayin zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, wanda ya yi nasarar lashe zaɓen 2023.
Tinubu ya doke sauran ‘yan takara 17, bayan ya samu ƙuri’u 8,794,726. Wato ƙuri’un sa sun fi na kowane ɗan takara yawa.
Sannan kuma ya samu kashi 25 bisa 100 a jihohi 30, fiye ma jihohi 24 da dokar zaɓe ta ce tilas sai wanda ya yi nasara ɗin ya samu.
Zaɓen ya nuna cewa Atiku da Obi da Kwankwaso su uku sun samu ƙuri’u milyan 14.5.
Hakan ya nuna kenan da a ce PDP ba ta rabu gida uku ba, za ta iya yin nasara kan APC a wannan zaɓe, domin har sun nunka APC yawan ƙuri’u su ukun.
Abin lura shi ne, sauran manyan ‘yan takara wato Atiku, Kwankwaso da Peter Obi duk rikicin jam’iyyya da rashin jin shawara ya raba su, kowa ya kama gaban sa, haɗin kai ya gagara, APC ta lashe zaɓe.
Dama Gwamnan Anambra, Charles Soludo ya ce Obi ba zai ci zaɓe ba, takarar sa alheri ce ga Tinubu na APC, domin Obi ya na ta ruguza PDP ce kawai.
“Da ni ne Tinubu har kuɗin kamfen ma sai na taimaka wa Obi da su. Saboda PDP ya ke yi wa illa, amma ba cin zaɓe zai yi ba.” Inji Soludo.
Shugaban INEC ya bayyana sakamakon zaɓe kusan asubahin ranar Laraba, ya ce Atiku Abubakar na PDP ne ya zo na biyu da ƙuri’u 6,984,520.
Peter Obi na LP ya zo na uku da ƙuriu 6,101,503, sai Rabi’u Kwankwaso na NNPP ya zo na huɗu da ƙuri’u 1,496,687.
Yakubu ya ce za a bai wa Tinubu satifiket na lashe zaɓe ƙarfe 3 na ranar Laraba a Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe.
Tinubu ya lashe Ribas, Barno, Jigawa, Zamfara, Benuwai, Kogi, Kwara, Neja, Osun, Ekiti, Ondo, Oyo da Ogun.
Atiku ya lashe Katsina, Kebbi, Sokoto, Gombe, Yobe, Bauchi, Taraba, Adamawa da Akwa Ibom, Osun da Bayelsa.
Peter Obi ya lashe Cross Riba, Delta, Legas, FCT, Filato, Imo, Ebonyi, Nasarawa, Anambra, Abiya, da Enugu.
Kwankwaso kuma ya lashe Kano kaɗai.