Ƙaramin Ministan Ƙwadago, Festus Keyamo ya rubuta wa SSS wasiƙar roƙon su kama ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi da mataimakin takarar sa, Datti Baba-Ahmed, saboda kakkausan furucin da ya ce sun yi izgilanci kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2023.
Keyamo wanda ya yi wa Rundunar Yaƙin Shugaban Ƙasa na APC Kakakin Yaɗa Labarai, ya rubuta wasiƙar s ranar 23 Ga Maris,
Ya ce Obi da Datti sun yi kalaman da ka iya tunzira jama’a kan gwamanti da kuma zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu.
Premium Times Hausa ta buga labarin hirar da aka yi da Datti a gidan talabijin na Channels TV, inda ya ce, ‘Babu zaɓaɓɓen shugaban ƙasa a Najeriya’.
Ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa na jam’iyyar LP, Datti Baba-Ahmed, ya bayyana cewa “Najeriya ba ta da zaɓaɓɓen shugaban ƙasa.
A cikin wata tattaunawa da aka yi da shi ranar Litinin a Gidan Talbijin na Channels, ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari da kuma gargaɗi ga Cif Jojin Najeriya, Olukayode Ariwoola kada ma su halarci Dandalin Eagle Square wurin rantsar da Tinubu, saboda babu ma dalilin yin taron ballantana rantsarwar.
Datti ya ce taron ranar 29 Ga Mayu domin rantsar da Tinubu da Shettima haramtacce ne idan ma sun ce za su yi, saboda takarar Tinubu da ta Shettima duk haramtattu ne.
Ya ce shi dai Tinubu bai cika sharuɗɗan da doka ta gindiya ba kafin a bayyana shi wanda ya yi nasara.
“Saboda dokar ƙasa ta bayyana cewa sai ɗan takara ya ci jihohi 24 da Gundumar FCT Abuja tukunna, sannan za a ce ya ci zaɓe. Shi kuwa Tinubu bai ci FCT Abuja ɗin ba.
Daga nan ya yi wa Cif Jojin Najeriya jan-hankalin cewa kada shiga shirgin rantsar da Tinubu da Shettima, domin haramtattun ‘yan takara ne.
Ya ce INEC ce ta yi shirme da gangancin bayyana bayyana Tinubu da Shettima waɗanda su ka yi nasara, alhali ba su yi ɗin ba, sannan kuma takarar su haramtacciya ce, har aka yi gangancin damƙa masu satifiket na lashe zaɓe.
“Karya doka ce a rantsar da wanda bai cika sharuɗɗan dokar cin zaɓe ba. Yin hakan tamkar komawa ce a mulkin soja. Duk wanda ya rantsar da wanda bai cancanta ba, ya karya doka. Kuma ba su cancanta zama shugabanni ba.” Cewar Datti.
Ya ce tuni ya daina tunanin adalci a kotun Najeriya, tun daga lokacin da Kotun Ƙoli ta bai wa Sanata Ahmad Lawan takarar sanata, alhali kuwa ya karya doka.
“Doka ta hana ɗan takara fitowa takara fiye da ɗaya a lokaci guda. Amma Sanata Lawan ya fito takarar shugaban ƙasa, kuma ya fito takarar sanata duk a lokaci guda. Wannan kuwa ya karya doka.
“Ni da farko ai na fito takarar sanata a Kaduna, amma da aka ce na fito takarar mataimakin shugaban ƙasa, sai na janye takarar sanatan da na je yi.” Inji Datti.