Idan ba a manta ba tun bayan kammala zaɓen shugaban kasa sa a ka yi ranar 25 ga Faburairu, shugabanni da magoya bayan jam’iyyar NNPP mai alamar kayan daɗi ta ke ta mika kukan ta ga mahukunta cewa ana kokarin haɗa baki da gwamnatin jihar da jami’an tsaro domin a muzguna wa magoya bayanta a zaɓen jihar Kano.
Wannan korafi da zarge-zarge da NNPP ke yi sun haɗa da kokarin canja Kwamishinan ƴan sandan jihar da aka yi domin a cewar su a kawo wanda zai baiwa jam’iyya mai mulki haɗin kai a yi murɗiya a Zaɓen gwamnan jihar.
A ranar Alhamis, rundunar SSS ta kama wasu magoya bayan jam’iyyar NNPP wanda ɗaya daga cikin su limamin masallaci a Wudil mai suna Isma’il Mangu sai kuma wani mawaƙin Kwankwasiyya mai suna Abubakar Tabula wanda shima a ka kama bisa zargin wai ya yi waƙa da zai iya ingiza mutane a samu tashin hankali a jihar.
Kakakin rundunar SSS Peter Afunanya ya ce an kama Tabula da Mangu bisa zargin yin kalaman da zai iya ingiza mutane a samu tashin hankali a zaɓen ranar Asabar.
A cikin kalaman da liman Mangu ya yi wanda aka ɗauka aka rika raba wa mutane a shafukan sada zumunta, wato a yanar gizo, an ji muryarsa yana cewa kada mutane su kuskura su bari a murɗr musu zaɓen, gwamna, idan za su kwana ne su kwana a ofishin zaɓe. ” Kowa ya dafo abinci ya zo da shi ba za mu yarda da ‘Inkwankulosib’ ba.
Waɗannan da wasu kalamai ne da ake zargi sa da furtawa a wurin Huɗubar suka sa aka kama shi da mawaki Tabula, aka tsare.
A ƙarshe, hukumar SSS ta gargaɗi ƴan siyasa da magoya bayan su su kiyaye daga faɗin kalamai da maganganun da za su iya tada zaune tsaye a wannan lokaci na siyasa.