Akwai muhimman batutuwa da dama dangane da zaɓen Gwamnoni da na ‘Yan Majalisar Jihohi.
1. A jihohi 28 ne za a yi zaɓen gwamna, ba jihohi 36 na ƙasar nan ba.
2. Gwamnoni 11 ne masu fafurikar ganin sun yi tazarce, wato nasarar neman yin zango na biyu.
3. A jihohi 17 ne masu sabbin ‘yan takara baki ɗaya, wato ba tare da gwamnan da ke kai ya fito takara ba. Saboda gwamnonin jihohin sun kammala wa’adin su na zango na biyu.
4. Za a gudanar da zaɓe a mazaɓu 1,021 a ƙasar nan.
5. Za a zaɓi ‘yan majalisar jihohi har guda 993.
6. Jihohin da ba a za a yi zaɓen gwamna ba, sun haɗa da: Bayelsa, Edo, Ekiti, Imo, Kogi, Ondo da Osun.
7. Sai a cikin watan Nuwamba ne za a yi zaɓen gwamnoni a Kogi, Bayelsa da Imo.
8. FCT Abuja: Ba za a yi zaɓe a Gundumar FCT Abuja ba, saboda ba ta da gwamna kuma ba ta da ‘yan majalisa.
9. Za a kafsa takarar zaɓen gwamnoni tsakanin ‘yan takara fiye da 400 daga jam’iyyu 18.
10. Jihohin Abiya, Akwa Ibom, Filato da Taraba sun fi sauran jihohi yawan ‘yan takarar gwamna. Saboda kowace jam’iyyya ta tsayar da ɗan takara a jihohin.
11. Jihohin Kano, Enugu, Delta, Ribas da Sokoto kuwa jam’iyyu 17 ne su ka fito takarar gwamna.
12. Jihohin Cross River da Yobe ne masu ƙarancin ‘yan takara, inda jam’iyyu 11 kaɗai su ka tsayar da ‘yan takara.
12. Dukkan ‘yan takarar sun fito ne bayan sun ci zaɓen fidda gwani. Da yawa a cikin su kuma sai da aka dangana da kotu. Ɗan takarar PDP na Abiya ne kaɗai bai yi zaɓen fidda gwani ba, saboda daga baya aka bayar da sunan sa, bayan rasuwar ɗan takarar da ya yi nasara a zaɓen fidda gwani.
13. Jihohin da gwamnonin su ke haƙilon yin tazarce su 11, sun haɗa da Adamawa, Bauchi, Barno, Gombe, Legas, Kwara, Nasarawa, Ogun, Oyo, Yobe da Zamfara.
14. Jihohi 17 da gwamnonin su ba za su yi takarar a zaɓen, sun haɗa da: Abiya, Akwa Ibom, Benuwai, Cross Riba, Delta, Ebonyi, Enugu, Jigawa, Kaduna, Kano, Katsina, Kebbi, Neja, Filato, Ribas, Sokoto da Taraba.
‘Yan Majalisar Jihohi:
15. ‘Yan takara 10,231 ke neman kujerun Majalisar Jihohi 993 a faɗin jihohi 36.
16. Jihohin Kano da Legas ke da mafi yawan kujerun Majalisar Dokoki. Kowacen su na da 40. Sai Katsina mai 34, Oyo da Ribas kowace 32, Bauchi da Kaduna kowace 31, Benuwai, Jigawa, Anambra da Sokoto kowace 30. Akwai jihohi 13 masu kujeru 24 kowace.
17: Zaɓen Gwamnoni: Jihohin Da Za A Fi Yin Gwagwagwa Da Gumurzu: Masu nazari na ganin za a fi yin gwagwagwar zaɓe a jihohin Legas, Kano, Oyo, Adamawa, Nasarawa, Bauchi, Delta da Ribas.