An gudanar da zaɓen gwamnoni a jihohi 28. A cikin su gwamnoni 11 a zangon farko su ke, amma duk sun nemi zango na biyu.
Sannan akwai gwamnoni 17 waɗanda sun kammala wa’adin su na shekara takwas idan 29 ga Mayu ta zo.
Gwamnoni 17 Waɗanda Sun Kammala Wa’adin Su:
1. Nysome Wike, Gwamnan Ribas.
Ya ɗora makusancin sa Siminaliayi Fubara, kuma ya yi nasarar zama zaɓaɓɓen gwamna.
2. Okezie Ikpeazu, Gwamnan Abiya. An bayyana zaɓen jihar ‘Inkwankilusib’.
3. Ben Ayade, Gwamnan Cross Riba.
Ben Ayade Gwamnan APC ne da zai kammala zangon sa na biyu. Kuma ɗan takarar sa Bassey Otu shi ya yi nasara.
4. Udom Emmanuel, Gwamnan Akwa Ibom. Ɗan PDP ne, kuma wanda ,ai gaje shi a ranar 29 Ga Mayu, ɗan PDP ne, Umo Eno.
5. Ifeanyi Okowa Gwamnan Delta. Ɗan PDP ne da ya yi takarar mataimakin shugaban ƙasa ga Atiku Abubakar a PDP.
Wanda zai gaji Okowa ɗan PDP ne, kuma yanzu haka shi ne Kakakin Majalisar Dokokin Jihar Delta, wato Sheriff Oborevwori. Shi ya kayar da Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Ovie Omo-Agege na APC a zaɓen gwamna.
6. Ifeanyi Ugwuanyi ɗan PDP Gwamnan Enugu. Zaɓen Jihar ya zama ‘inkwankilusib’.
7. Dave Umahi, Gwamnan Ebonyi. Ɗan APC wanda zaɓaɓɓen gwamnan APC Francis Nwifuru zai gaje shi.
8. Aminu Masari Gwamnan Katsina. Masari ɗan APC ne, kuma Dikko Raɗɗa ɗan APC zai gaje shi.
9. Samuel Ortom Gwamnan Filato. Ɗan PDP ne, kuma ɗan APC, Rabaran Hyacinth Alia ne zai gaje shi. Ortom ya fito takarar sanata, amma ɗan aikin sa ya kayar da shi.
10. Nasiru El-Rufai Gwamnan Kaduna. Ɗan APC ne, kuma Uba Sani na APC ne zai gaje shi.
11. Abubakar Badaru Gwamnan Jigawa. Ɗan APC ne, kuma Namadi Ɗandodi na APC ne zai gaje shi.
12. Aminu Tambuwal Gwamnan Sokoto. Ɗan PDP ne, amma tsohon mataimakin sa ne ya yi nasara a APC, kuma shi zai gaje shi.
13. Bello Matawalle, Gwamnan Zamfara. Ɗan APC, amma Lawal Dare na APC ya yi nasara, kuma shi kai zai gaje shi.
14. Abubakar Bagudu Gwamnan Kebbi. Ɗan PDP ne, amma zaɓen jihar ya zama ‘inkwankilusib’.
15. Abdullahi Ganduje Gwamnan Kano. Ya kammala wa’adin sa, kuma ɗan takarar sa Nasiru Gawuna bai yi nasara ba. Abba Yusuf na NNPP ne ya yi nasara, shi ne zai gaje shi.
15. Abubakar Sani Bello Gwamnan Kebbi. Ɗan APC ne, kuma ɗan APC zai gaje shi, wato Umar Bago.
17. Darus Ishaku Gaamnan Taraba. Ɗan PDP ne, kuma Kefas Agbu na PDP zai gaje shi, kamar yadda INEC ya bayyana sakamakon zaɓen gwamnan jihar.