Yayin da ake ci gaba da jefa ƙuri’a, Gwamnan Jihar Sokoto Aminu Tambuwal ya jinjina wa yadda Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ke gudanar da zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi a cikin tsari.
Shi kuwa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi, ya yi alƙawarin cewa duk yadda sakamakon zaɓe ya kaya, amshi ƙaddara, ko nasara ko rashin nasara.
Shi kuwa Gwamna Charles Soludo na Anambra da Godwin Obaseki na Edo da kuma Shugaban APC na Ƙasa, Abdullahi Adamu, sun nuna damuwar su ce dangane da rashin fitowar masu jefa ƙuri’a da yawa a zaɓen na yau Asabar.
Dama kuma wasu rahotanni sun bayyana a Jihar Ribas ma da wasu wuraren duk an yi ƙorafin rashin fitowar jama’a da yawa domin su jefa ƙuri’a.
Wani rahoton kuma ya nuna a jihar Kano an fito sosai, kuma tun ƙarfe 6 na safiya wasu matasa da dama su ka shiga layin tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe.
A yawancin unguwannin cikin Kano, har ƙarfe 12 na ranar zaɓe ana ta raba wa talakawa taliya da atamfofi.
Yayin da jama’a da dama su ka fita domin su je rumfar zaɓe su shiga layin jefa ƙuri’a tun bayan Sallar Asubahi a Kano, a gefe ɗaya kuma jam’iyyar APC a jihar ta bazama ta na ci gaba da rabon atamfofi da taliya domin jama’a su zaɓi ɗan takarar ta, Nasiru Yusuf Gawuna.
Gawuna wanda shi ne Mataimakin Gwamna Abdullahi Ganduje, ya na fuskantar babbar barazana daga ɗan takarar gwamna na NNPP, Abba Kabiru Yusuf, wanda aka fi sani da Abba Gida-gida.
Tun a zaɓen shugaban ƙasa dai NNPP ta nuna da gaske ta ke yi sai ta ƙwace kujerar gwamna daga APC.
A zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, NNPP ta samu sanata biyu a Kano, ciki har da Sanatan Kano ta Tsakiya, Rufai Hanga, wanda ya samu ƙuri’a 457,787, kuma shi ne ya fi kowane sanata na ƙasar nan yawan ƙuri’u.
NNPP na da ɗan majalisar tarayya 18, ita kuma APC na da guda 5 kaɗai.
Wasu bayanai sun nuna cewa ita ma NNPP ta na rabon taliya, to amma dai wakilin mu bai tabbatar da wanda ya ce ya karɓa ba.
“Tun ɗazu na je Rumfar Zaɓe ta Firamaren Ɗandago a cikin Kano. Amma ina komawa gida ƙarfe 11:05 na tarar a layin mu, wato Lokon’ Gawo ana raba atamfa da taliyar Gawuna.” Inji wani da ba ya so a ambaci sunan sa.
Tuni dai atamfofi da tsakiyar Gawuna su ka cika soshiyal midiya. Wasu na godiya, wasu kuma na cewa sun karɓi atamfa, amma NNPP za su zaɓa.