Hukumar EFCC ta ce ta yi nasarar damƙe fiye da mutum 65 a lokacin da su ke ƙoƙarin sayen ƙuri’u a jihohi 28 waɗanda aka gudanar da zaɓen gwamnan jiha da na majalisar jihohi.
Wadanda ta damƙe ɗin a wurare daban-daban a ranar zaɓe, an kama 20 a Shiyyar Ilorin, wasu 13 kuma an kama su ne a wuraren gudanar da zaɓe guda a Shiyyar Kaduna.
Wani da ake zargi da sayen ƙuri’u an damƙe shi a Rumfar Zaɓen Unguwar Rimi, Kaduna.
Da farko ya yi tirjiyar ƙin yarda a kama shi, amma dai a yanzu ya na hannun EFCC kafin a kammala bincike.
Har yau a Kaduna an kama wani mai suna Esmond Garba a Unguwar Dogara Yaro Dagari, an same shi da takardun killace alƙaluman zaɓe.
A Fatakwal an damƙe mutum 12 sai Shiyyar Uyo inda aka kama mutum huɗu a Kalaba.
Sauran masu sayen ƙuri’u kuma an kama ai a Gombe, Sokoto.
Mutum 20 da aka damƙe a Shiyyar Ilorin sun haɗa da Adekunle Ademola, Wasiu Raimi, Laaro Rasheed, Alegbe Taiwo, Boniface Victory, Kayode Toba, Adeoye Adetunji, Lawal Favour, Abidoye Victoria, Magaji Iliasu, Abdulƙadir Abdulmumin da Musa Lateef da sauran su.
Yayin da a jihar Gombe mutum 10, an kuma kama kuɗaɗe a hannun su.