Baturen Zaɓe Farfesa Tusuf Saidu ya ce an soke zaɓe a wurare da dama a kananan hukumomi 20 cikin 21 a jihar, wanda ya fi yawan banbancin kuri’un da jam’yy da ta yi nasara ke da shi.
Bi sa ga sakamakon zaɓen jam’iyar ta samu 388,258 ita kuma PDP 342,980.
Banbancin kuri’un dake tsakanin su 45,278. Amma kuma da muka hada yawan kuri’un da aka soke sun zarce 90,000. Dalilin haka ya sa dole sai an sake zaɓe a wadannan wurare domin a iya samun wanda yayi nasara kamar yadda doka ta ce.