Ɗan takarar gwamnan Kano na APC, Nasiru Yusuf Gawuna, wanda ya sha kaye a hannun Abba Kabir Yusuf na NNPP, ya bayyana cewa ya daina jayayya da nasarar da Abba ya samu, kuma ya taya shi murna.
Cikin wani faifan murya da ya fitar a yau Laraba, 29 ga Maris, Gawuna ya ce ya rungumi ƙaddara, tare da taya Gida-gida murna da yi masa addu’ar fatan alheri.
Sannan kuma ya yi kira ga zaɓaɓɓen gwamnan ya yi shugabanci na adalci, yayin da ya ce zasu yi fatan ya kawo ci gaba a jihar Kano.
Gawuna wanda ke magana a cikin sanyin murya, ya roƙi magoya bayan sa cewa su ma su rungumi ƙaddara, kuma su yi wa zaɓaɓɓen gwamnan fatan alheri.
“Dama tun kafin zaɓe mun yi addu’a cewa Allah ya zaɓa mana mafi alheri. Idan mulkin zai zama alheri a wurin mu, to Allah ya ba mu. Idan kuma ba zai zama alheri ba, to Allah ka musanya mana da mafi alheri. Saboda haka a yau 29 ga Maris, 2023, ni Nasiru Yusuf Gawuna na rungumi ƙaddara.” Haka ya faɗa a cikin muryar wadda ke ɗauke da jawabin sa na minti 2 da sakan 15.