Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna na Jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani ya yi alƙawarin sharewa mutanen Kaduna hawaye tare da zama tare da su a koda yaushe domin shawarwari da share muku hawaye.
Hakan na kunshe ne a jawabin da yayi wa mutanen Kaduna ranar Alhamis domin neman goyon bayan su a zaɓen gwamna da za a yi ranar Asabar.
Uba ya ce ba shi da nuna wariya ta kabilanci ko addini.
” Na bayyana a gareku ne mutanen jihar Kaduna domin rokon ku ku mara mini baya ku zaɓe ni gwamnan Kaduna a zaɓen da za ayi ranar 18 ga Maris.
” Ina tabbatar muku cewa zan zama ga kowani ɗan jihar Kaduna adalin gwamnan da zai share muku hawaye. Sannan kuma zan saurare ku da duk wani shawarwari da zaku zo min da shi a koda yaushe a matsayi na na gwamnan jihar Kaduna idan kuka zaɓeni, InshaAllah.
” Na zo gare ku a matsayin ɗaya daga cikin ku wanda ya yi gwagwarmayar tabbatar da ƴanci tare da tabbatar da ganin cewa talakawan jihar Kaduna sun sami daidaituwa tare da samun wataya a duk harkokin su da wanzuwar ci gaba a ayyukan su da sana’o’in su.
A karshe sanata Uba ya ce burin sa shine ya ga alummar da musamman talakawar jihar Kaduna sun sami kwanciyar hankali da natsuwa a harkokin su da zamantakewa ba tare da nuna banban ci ba.
Discussion about this post