Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta bayyana adadin sanatoci da wakilan majalisar ƙasa na jam’iyyun da su ka samu wakilci a zaɓen ranar 25 Ga Fabrairu.
Jam’iyyar APC ta samu lashe kujerar sanata guda 57, sai wakilan majalisar ƙasa 162.
INEC ta ce ta fitar da sakamakon zaɓen kujeru 423, waɗanda PDP da LP ke biye da APC a yawan sanatoci da wakilan.
Shugaban Hukumar Zaɓe ta Kasa, Farfesa Mahmood Yakubu ne ya bayyana haka ranar Asabar a Abuja, lokacin da ya ke jawabi wurin taron da INEC ta yi da Kwamishinonin Zaɓe da kuma jam’iyyu takwas da ke da wakilci a majalisar tarayya.
Jam’iyyun takwas su ne APC, PDP, APGA, SDP, LPZ, NNPP, ADC da YPP.
Yakubu ya ce an kammala zaɓen kujerar wakilan majalisa 423 daga cikin 469.
Ya ce a majalisar dattawa an kammala zaɓen sanstoci 98 daga cikin 109 da ake da su.
Daga cikin mambobin majalisar wakilai ta ƙasa kuwa su 360, an kammala zaben 325.
Shugaban na INEC ya ce APC ce mai Sanatoci 57, sai PDP mai 29.
Yayin da LP mai Sanatoci 6, NNPP da SDP kowace biyu, APGA da YPP kuma kowace sanata ɗaya.
A majalisar wakilai ta ƙasa kuwa, APC na da wakilai 162, PDP kuma 102. LP na da wakilai 34, NNPP na da 18, AFGA huɗu, ADC da SDP kowace biyu, sai YPP wakili ɗaya.
Yayin da APC ke da mafi yawan wakilan sanatoci, a Majalisar Ƙasa kuwa ta kasa samun haka, saboda doka ta ce jam’iyyya ba za ta zama mai rinjaye a majalisa ba, sai ta na da wakilai 180 cif.
Yakubu ya ce za a yi zaɓuka a mazaɓu 46 domin kammala wakilan sanatoci da na wakilan ƙasa.
Daga nan ya ce a ranar 7 Ga Maris za a bai wa dukkan wakilan satifiket ɗin su.