Zaɓaɓɓen shugaban ƙasa, Bola Tinubu, ya ce zaɓen sa da a ka yi a ranar 25 ga Fabrairu, an yi adalci, kuma babu maguɗi, sannan sahihin zaɓe ne da babu wata tangarɗa a tare da shi.
Tinubu ya ce zai kafa gwamnatin da ba zai tsaya naɗa muƙamai a cikin ‘jam’iyyar sa kaɗai ba.
Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis, ya ce zai kafa “gwamnati ta mutanen da su ka cancanta.”
“Ana ta magana cewa za a kafa gwamnati ta haɗin kan ƙasa. To ni buri na ya ma wuce haka. Zan kafa gwamnati ta hanyar naɗa mutanen da su ka cancanta a kan muƙaman da za a naɗa su. Ba zan dubi alaƙa ta ko kusancin siyasa ta da mutum na ɗauko shi na naɗa shi kan muƙami ba. Ni cancanta zan duba da kuma abin da mutum ya shuka na nagarta da cancanta a baya,” inji Tinubu.
Tinubu dai ya samu ƙuri’u miliyan 8.7, inda ya yi nasara kan sauran ‘yan takara 17, cikin su har da Atiku Abubakar wanda ya zo na biyu, da kuma Peter Obi wanda ya zo na uku.
Sai dai kuma PDP da Atiku, LP da Peter Obi duk sun ƙi amincewa da sakamakon zaben, kuma tuni su ka garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara, su ka shigar da ƙarar ƙin amincewa da sakamakon zaɓe wanda INEC ta fitar.
A cikin sanarwar da Tinubu ya fitar, ya ce ya yi nasara a “sahihin zaɓen da aka gudanar,” sai dai kuma ya ce ‘yan takara masu jayayya na da ‘yancin garzayawa kotu.
Ana jiran ranar da 29 ga Mayu domin a rantsar da Tinubu, ko da shari’ar masu jayayya da shi a kotu ko babu.
Discussion about this post