Yunƙurin da wasu ‘Yan Majalisar Wakilai ta Ƙasa na APC su uku su ka yi domin ganin an kafa dokar da za ta halasta taba wiwi ya samu cikas a majalisa.
Honorabul Ben Kalu daga Abiya, Miriam Onuoha daga Imo da kuma Olumide Osoba daga Ogun ne su ka haɗu su ka gabatar da wani ƙudiri, wanda su ke so a yi wa Dokar NDLEA kwaskwarima, domin a halasta noman ganyen taba wiwi.
Su na so ne a halasta noma ganyen wiwi don a riƙa amfani da shi wajen haɗa magunguna da sauran ababen da za su amfani mutane.
Haka nan kuma, ƙudirin na su ya nemi a bai wa Hukumar Hana Tu’ammali da Muggan Ƙwayoyi (NDLEA) ikon bada lasisi da kuma ikon soke lasisin noma ganyen taba wiwi, wacce akasari kala uku ce, kamar yadda su ka yi bayani.
Su na so ikon noma ganyen taba da ikon ƙwace lasisin noman ta ya koma kan Hukumar NDLEA.
Nau’in tabar wiwi ɗin da su ke magana a kai ya haɗa da ‘Cannabis Sativa’, ‘Cannabis Indicia’ da kuma ‘Cannabis Ruderalis’. Dukkanin su dai wiwi ce mai sa mashayin ta tangaɗi, layi, magaro da kuma gushewar hankali.
Da ya ke jagorantar ce-ce-ku-ce kan batun halasta tabar wiwi a Majalisa, Ben Kalu ya ce idan Najeriya ta halasta noman ganyen taba wiwi, za ta samu damar shiga ƙungiyar ƙasashen da su ka haɗa da Ajantina, Austaraliya, Kanada, Chile, Colombiya, Croatia da Cyprus, waɗanda su ka halasta noman tabar wiwi ana amfani da ganyen wajen kula da masu fama da ciwon sankarar daji, wato ‘cancer’.
Ya ce wannan ƙudiri ba wani kuɗi zai ƙara ci wa gwamnatin tarayya ba, saboda dama akwai Hukumar NDLEA, wadda a ƙarƙashin ta kula da ƙa’idojin noma da amfani da wiwi ɗin zai kasance.
Sai dai kuma ‘yan majalisa da dama irin su Nicholas Ossai, ɗan PDP daga Delta ya ce bai yiwuwa Najeriya ta halasta noman tabar wiwi, a lokacin da ta ke gaganiyar neman yadda za ta daƙile illar da tabar ke ci gaba da yi wa musamman matasa a ƙasar nan.
“Crystal meth ya illata matasan Kudu maso Gabas, sannan kuma wani yanzu ya zo ya ce wai a halasta wiwi? Ba za mu yarda ba.” Inji Ossai.
Ossai ya ce har yanzu babu wani sahihi kuma karɓaɓɓen binciken da masana su ka gano cewa tabar wiwi na da amfani da jikin mutane.
Sai dai kuma Kakakin Majalisar Tarayya, Femi Gbajabiamila ya bai wa Ossai amsa da cewa masana ne su ka fi cancanta su yanke hukuncin alfanun wiwi ko rashin alfanun ta a jikin mutane, idan har za a yi zaman sauraren ra’ayoyin jama’a.
Mambobi irin su Mataimakin Kakakin Majalisa, Idris Wase, Uzoma Abonta, da Mohammed Monguno duk sun ƙi amincewa da ƙudirin.
Ita kuwa Onuoha, wacce har da ita cikin waɗanda su ka gabatar da ƙudirin, ta ce ba dukkan nau’in taba wiwi ke sa cakewa ba.
Daga nan dai da ta ga an ƙi amincewa, sai ta nemi ta janye ƙudirin har sai nan gaba idan dama ta sake bayar da gabatar da shi.
Nan take kuwa ta janye ƙudirin, aka daina maganar, aka wuce wurin.