Babbar Kotun Tarayya da ke Bauchi ta ɗaure wasu gaggan ‘yan jam’iyyar PDP biyu na Jihar Bauchi.
Ta kama su da laifin yunƙurin yin amfani da Naira miliyan 142 domin su sayi sakamakon zaɓe a lokacin zaɓen. 2015 a Bauchi.
EFCC ce ta gurfanar da gaggan ‘yan PDP ɗin su biyu, Saleh Gamawa da Aminu Gadiya bisa tuhumar su da laifin harƙallar karɓar Naira miliyan 142,460,000.00 da nufin dillancin murɗe sakamakon zaɓe.
A tuhuma ta biyu ma an gabatar da hujjojin uku kamar yadda aka gabatar da wasu hujjoji uku a tuhuma ta farko, waɗanda Mai Shari’a ya ce duk ya gamsu da hujjojin cewa waɗanda ake tuhumar sun aikata laifin da ake zargin sun aikata.
EFCC ta ce sun karɓi kuɗaɗen daga daga Ofishin Kamfen na PDP a hannun Daraktan Kuɗaɗe na kamfen ɗin a 2015 lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
Wanda ake tuhuma na farko dai ya roƙi kotu ta yi masa afuwa, domin a cewar sa, “akwai nauyin iyali masu ɗimbin yawa a kai na, ciki har da iyalin babban yaya na, wanda a yanzu ya makance, ni ke riƙe da iyalin na sa.
“Sannan kuma tun da aka fara shari’ar nan tsawon shekaru da dama, ko PDP ko gwamnati babu wadda ta tausaya mana ballanata ta kawo mana ɗauki.”
A tuhumar farko an ɗaure kowanen su shekara biyu ko tarar Naira miliyan uku.
A tuhuma ta biyu kuma an ɗaure Gadiya shekaru biyu a kurkuku ko tarar Naira miliyan uku.
Su biyun duka dai sun zaɓi biyan tarar maimakon zaman gidan kurkuku.
An dai fara wannan shari’a tun a ranar 4 ga Yuni, 2018.
Discussion about this post