Tsohon gwamnan Zamfara AbdulAziz Yari ya yi wa talakawa, miskinai da fakiran jihar Zamfara, ambaliyar abincin buda-baki da Sahur.
Yari ya shigo da kayan abinci har Tirela 240 domin tallafa wa muatne jihar musamman wadanda ba su da karfin ciyar da kansu da iyalan su.
Rabon da aka gudanar a ranar Lahadin da ta gabata a garin Talata-Mafara dake karamar hukumar Talata-Mafara, shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sen. Abdullahi Adamu, ya samu wakilcin shugaban jam’iyyar na yankin arewa maso gabas, Salihu Mustafa da shi ne ya kaddamar da rabon.
Ya ce daga cikin tireloli 240 na kayan abinci, za a raba 140 ga kananan hukumomin jihar 14, manyan motoci 10 kowace karamar hukumar.
” Za a raba Tirelolin abinci 32 a sansanonin ‘yan gudun hijira, Tireloli 12 kuma za a raba wa marayu ne suma su shaida, sannan za a raba wa kungiyoyi dabandaban tirelolin abinci 10, Tireloli 46 kuma na malamai ne masu karantar da addini da wasu matalauta a fadin jihar.
mataimakin gwamnan jihar Zamfara wanda ya wakilci gwamna Bello Matawalle a wajen rabon ya jinjina wa tsohon gwamnan bisa wannan abin alkhairi da yayi wa mutanen jiha Zamfara.