Rundunar ‘yan sandan jihar Ogun ta kama wani magidanci mai shekara 43 Abiodun Oladapo bisa zargin aikata laifin yi wa ‘yarsa mai shekara 19 ciki.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar Abimbola Oyeyemi ya sanar da haka ranar Asabar din da ta gabata a Abeokuta.
Oyeyemi ya ce ‘yan sanda sun kama Oladapo ranar Juma’a bayan karar da Oluwatoyin Idowu ya kawo a ofishin ‘yan sandan dake Mowe.
Ya ce Idowu ta bayyana wa jami’an tsaron cewa ta zo ta kawo kara yadda ake zargin dan ta Michael Idowu cewa shi ya yi wa yarinyar ciki bayan kuma ba shi bane.
“Idowu ta ce ta gano haka bayan tambayoyi da ta yi wa danta inda ta gano cewa kazafi ne kawai aka yi masa.
“Idowu ta ce Michael ya ce ya yi lalata da yarinyar a watan Disemba 2022 sannan zuwa yanzu cikin da take dauke da shi ya kai wata biyar amma yarinyar ta ce mahaifinta ne ya yi mata ciki ba Michael ba.
“Ta ce yarinyar ta ce tun a watan Fabrairu 2022 mafinta yake lalata da ita tare da yi mata barazanar zai kashe ta idan ta fada wa wani.
“Ta ce tun bayan da mahaifin ita yarinyar ya gano cewa tana da ciki ya tilasta ta tayi wa Michael sharrin cewa shine yayi mata cikin.
“DPOn ‘yan sandan dake Mowe ya sa a kamo mahaifin yarinyar inda a nan ne ya tabbatar wa ‘yan sanda cewa lallai shine ya dirka wa ‘yar sa ciki ba Michael ba.
“ Da ya shiga hannun ‘yan sanda Oladapo ya tabbatar cewa shine ya yi wa ‘yarsa ciki amma hudubar shaidan yabi ba da son ransa bane ya aikata hakan.