Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta bayyana cewa ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane ne sun kashe dagacen kauyen Maigari dake karamar hukumar Rimin Gado.
Maharan sun kashe Dahiru Abbas mai shekara 70 a cikin gidansa ranar Lahadi da safe.
Kakakin rundunar Abdullahi Haruna-Kiyawa ya sanar da haka a wani takarda da ya fitar ranar Lahadi.
“Da misalin karfe 3:05 na safiyar Lahadi rundunar ta samu rahoton cewa wasu ‘yan bindiga da ake zargin masu garkuwa da mutane sun afka gidan Abbas dagacen Maigari dake karamar hukumar Rimin Gado domin yin garkuwa da shi.
“Maharan sun harbe Abbas a kirji yayin da suke kokarin tafiya da shi sannan ya rasu yayin da likitoci ke duba shi a asibitin Murtala Muhammed dake garin Kano.
Haruna-Kiyawa ya ce rundunar ta fara gudanar da bincike domin kamo maharan da suka kashe dagacen.
Kamfanin Dillancin Labaran Najeriya NAN ta rawaito cewa Abbas shine mahaifin Shugaban karamar hukumar Rimin Gado Munir Dahiru-Maigari.
Discussion about this post