Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya gargaɗi duk wanda ke da korafi akan zaɓen da aka kammala na shugaban kasa ya gaggauta garzaya wa kotu kawai amma kada ya kuskura ya tada wa mutane hankali tunda wuri.
A wasikar taya sabon shugaban kasa murna da yayi shugaba Buhari ya ce wannan zaɓe ta bugu matuƙa domin idan aka yi dubi da yadda mutane suka yi zaɓe zai nuna maka cewa lallai kowa ya zaɓi abinda ya ke so ne, ba a tilasta masa ba.
” Ku duba ku gani, ninkai na na faɗi a jiha ta, haka shima ɗan takarar ya faɗi a jihar sa. Saboda haka zaɓe yayi kyau kuma kowa da ya san ciwon kan sa ya gamsu da sakamakon zaɓen.
” Eh lallai an samu ƴan matsalolin da ba a rasa ba, amma hakan ba zai sa a cewa wai shi kenan sai a rusa zaɓen gaba ɗaya ba, ko kuma a tada hankulan jama’a. Idan abinda aka yi bai gamsar da kai ba ka tattar korafe korafen ka ga garzaya kotu.
Daga nan sai ya taya Bola Tinubu murnar lashe zaɓen sannan ya bayyana cewa za su aiki tare wajen shirya yadda za a mika mulki ga sabuwar gwamnati.