Ɗan takarar gwamnan jihar Kaduna ƙarkashin APC, sanata Uba Sani ya yi alwashin kwarara atyukan ci gaba a masarautar da sauran masarautun dake wannan yanki.
Sanatan ya ziyarci masarautar ranar Lahadi, inda ya zarce kai tsaye zuwa fadar mai martaba sarkin Lere Suleiman Umaru.
A lokacin jawabin sa, Uba Sani ya jinjina wa mutanen karamar hukumar Lere bisa goyon baya da suke bashi ba tun yanzu ba.
” Karamar hukumar Lere, gida ne a wurina. A nan ne na yi karatu tare da wasu ƴan garin Lere waɗanda kusancin mu yasa mun zama kamar ƴan uwa.
” Duk ayyukan da zamu idan muka yi nasara ba za mu manta da wannan gari na Lere ba da kuma karamar hukumar baki ɗaya.
Bayan kammala jawabi, sai mai martaba sarkin Lere ya godewa ɗan takarar sannan ya yi masa fatan Alkhairi ga abin da ya saka a gaba.
PREMIUM TIMES HAUSA ta tattauna da Majikiran Lere, Ahmed Mohammed domin karin bayani game da wannan ziyara na sanata Uba ya yi.
majikira ya ce” Eh lallai wannan ziyara ce mai mahimman ci a garemu mutanen yankin Lere domin kuwa ba wannan bane karon farko da ɗan takaran ya ke ziyartar wannan yanki ba. Kuma kowa ya ga yadda aka amshe shi da tarba mai kyaun gaske da ya samu. Fatan mu shine Allah ya ida nufi.
Bayan masarautar Lere, Sanata ya kai irin wannan ziyara masarautun, Piriga, Saminaka da Kudaru kuma ya gana da sarakunan su da s’dul sun yi masa fatan alkhairi.
Discussion about this post