Dan takarar gwamna na jami’yyar APC a jihar Kaduna Uba Sani ya yi alkawarin gina sabbin cibiyoyin kiwon lafiya a matakin farko biyu a mazabu 255 dake jihar Kaduna domin amfanin jama’a.
Sani ya fadi haka ne a shirin gidan rediyon FRCN da aka yi da shi ranar Asabar a Kaduna inda a Shirin ya ke bayanin cewa gwamnan jihar Nasir El-Rufa’I ya yi namijin kokari gina cibiyar lafiya na matakin farko daya a kowace mazaba dake jihar.
Ya ce zai kara bisa aikin da gwamna El-Rufa’I ya Yi a jihar ta hanyar gina cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko biyu a kowace mazaba sannan zai zuba ingantattun kayan aiki da ma’aikata a cibiyoyin.
Idan ba a manta ba Sani ya sa baki domin gyara cibiyoyin lafiya guda bakwai a yankinsa na majalisar dattawa da ya shafi kananan hukumomin Kaduna ta Arewa, Kaduna ta Kudu, Kajuru, Chikun, Igabi da Giwa.
“A karamar hukumar Birnin Gwari na gina asibitin kula da mata tare da zuba kayan aiki na zamani.