Wani rahoton da aka fitar kwanan nan ya lissafa cewa tsagerun IPOB masu ƙumajin kafa ƙasar Biafra a Kudu maso Gabas ɗin Najeriya, su na cikin manyan ƙungiyoyin ‘yan ta’adda 20 na duniya.
Rahoton dai ƙungiyar ƙididdiga da bibiyan ayyukan ta’addanci a duniya, ‘Global Terrorism Index’ (GTI) ce ta fitar da shi a 2023.
Yayin da Najeriya kuma ita ce ƙasa ta takwas a duniya, a jerin ƙasashen da ‘yan ta’adda su ka fi yi wa illa a 2022, kamar yadda rahoton ya bayyana.
A rahoton baya kafin wannan dai Najeriya ce ƙasa ta shida, wadda ta fi fama da ta’addanci. Kuma a wannan matsayin ta ke fiye da shekaru uku da su ka gabata.
Tsawon shekaru huɗu kenan a jere ana lissafa Afghanistan a matsayin ƙasa ta farko, wadda ta’addanci ya fi mamayewa, kuma ya yi mata mummunar illa.
Daga Afghanistan sai ƙasashe uku a jere duk na Afrika, waɗanda su ka haɗa da Burkina Faso ta biyu, Somaliya ta uku, Mali ta huɗu.
Ƙasar Siriya ce ta biyar, sai Pakistan ta shida, ita kuma Iraƙi ta bakwai.
Bayan Najeriya na matsayin takwas, Myanmar ce mai bi mata, wato ta tara.
Ta goma ita ce Jamhuriyar Nijar, wannan ƙungiya dai wadda ta fito da ƙididdigar jadawalin, ta wasu ƙwararrun masana ne a Sydney, babban birnin Austaraliya.
GTI ya ɗora IPOB matsayin hatsabiban ‘yan ta’adda na goma a duniya, yayin da ISIS masu ta’addanci tsakanin Iraq da Siriya ke na ɗaya a ƙololuwar ta’addanci a duniya.
ISWA da ke ɓarna a Afrika ta Yamma ita ce ta shida, kuma ta na ta’addanci ne musamman a cikin Najeriya.
Daga nan sai Boko Haram wadda ita ce ta bakwai.
Cikin 2017 ne Gwamnatin Najeriya ta ayyana IPOB matsayin ƙungiyar ‘yan ta’adda.
IPOB ta kashe mutum 57 kuka ta kai munanan hare-haren sau 40 duk a cikin 2022.