Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa, Bola Tinubu ya sheƙa birnin Paris da Landan, domin yin hutun jigatar kamfen ɗin zaɓen shugaban ƙasa.
Asiwaju ya bar Najeriya a ranar Talata, inda daga can kuma zai zarce Umrah a Makka, Saudi Arabiya.
Zai je Paris da Landan ne ya huta, sannan kuma zai yi nazarin tsarin karɓar mulki daga gwamnati mai barin gado, wadda wa’adin ta zai ƙare a ranar 29 Ga Mayu, 2023, ranar da za a rantsar da Tinubu ɗin.
Kakakin Yaɗa Labaran Tinubu, Tunde Rahman, ya ce Tinubu ya bar Najeriya ta filin jirgin saman Murtala Mohammed da ke Ikeja, Lagos a ranar Talata da dare.
Rahman ya ce Tinubu zai tafi ya huta daga jigatar da ya yi wajen karakainar yawon kamfen ɗin takarar shugaban ƙasa.
“Zai huta a Paris da Landan, daga can kuma ya je Umrah Saudi Arabiya. Kuma a can zai fara azumin Ramadan, wanda za a fara ranar Alhamis.
“A can ne kuma zai samu natsatstsen lokacin da zai tsara shirin karɓar mulki. Ana tsammanin dawowar sa ƙasar nan da wuri, inji Rahman.
Yawan fitar da Tinubu ke yi ba zato ba tsammani ta na ƙara sa mutane da dama na tababar cikakkar lafiyar sa. Saboda ya sha fita zuwa Landan da Paris kafin a fara kamfen na zaɓen shugaban ƙasa.
Discussion about this post