Rukunin wasu daga cikin manyan malaman Kaduna sun yi buɗe baki da zaɓaɓɓen gwamnan Kaduna Sanata Uba Sani.
An gudanar da wannan taro na buɗe baki ne a garin Kaduna ranar Juma’a.
A wurin wannan taron wanda malamai suka halarta ranar Juma’a, sanata Uba Sani ya godewa duka malaman bisa wannan karramawa da suka yi masa yana mai cewa zai yi aiki tukuru don kawo sauye sauye masu ma’ana a faɗin jihar.
A jawabin sa Sanata Uba ya ce, ” Wannan karramawa da kuka yi min abu ne mai mahimmanci kuma ina godiya matuka. Ba zan ba mara ɗa kunya ba a jihar Kaduna sannan kuma nasarar da na samu nuni ne cewa mutane na son ci gaba da ragargazar kyawawan ayyukan da gwamnatin ke yi wanda akan turbar haka za mu ɗora domin amfanin mutanen jihar mu.
Malamai da dama su yi magana a wurin wannan taro inda suka tofa albarkacin bakunan su game da nasarar da Uba Sani ya samu da yi masa luguden addu’o’i fatan alkhairi.
Discussion about this post