Sakamakon zaɓen Jihar Taraba ya tabbatar da nasara kan Kefas Agbu, ɗan takarar PDP da yawan ƙuri’u 302,614.
Ya doke wanda ya zo na biyu, Muhammad Yahaya na NNPP wanda ya samu ƙuri’u 202,277.
Agbu dai tsohon soja ne da ya yi ritaya ya na Laftanar Kanar.
A Jalingo babban birnin Jihar Taraba INEC ta bayyana sakamakon zaɓen.
A jihar Zamfara kuwa, Dauda Lawan na PDP ya kifar da Gwamna Matawalle da rundunar yaƙin sa baki ɗaya.
Sakamakon zaɓen Gwamnan Jihar Zamfara da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa, INEC ta bayyana, ya tabbatar da cewa Dauda Lawal na jam’iyyar PDP ne ya yi nasara, inda ya kayar da Gwamna Bello Matawalle na APC.
Dauda Lawal ya samu ƙuri’u 377,726, shi kuma Gwamna Bello Matawalle ya samu 311,976.
Baturen Zaɓe Kashim Shehu daga Jami’ar Tarayya ta Birnin Kebbi ne ya bayyana sakamakon zaɓen a safiyar Talata a Gusau, babban birnin Jihar Zamfara.
Lawan ya yi nasara a ƙananan hukumomi 10 shi kuma Matawalle a ƙananan hukumomi huɗu.
Dauda ya yi nasara a Anka, Bukkuyum, Shinkafi, Gusau, Tsafe, Gummi, Bunguɗu, Maru, Kaura Namoda da kuma Zurmi.
Shi kuma Matawalle ya samu Maradun, Talata Mafara, Birnin Magaji da Bakura.
Matawalle dai ya ci zaɓe ne a 2019 a ƙarƙashin PDP, amma bayan ya hau mulki sai ya koma APC shi da jama’ar sa.
Mataimakin sa Aliyu ya ƙi bin sa, sai ya kitsa tuggun da aka tsige shi.
A yanzu kuma Aliyu ya haɗa kai da Dauda Lawan, an yi nasara kan Gwamna Matawalle. Haka shi ma Kakakin Majalisar da ya jagoranci tsige Aliyu Mataimakin Gwamna a lokacin, shi ma a yanzu ya faɗi zaɓe, PDP ta kayar da shi.
Discussion about this post