Gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari ta ce ta kashe sama da naira biliyan 35 wajen azurta al’ummar Jihar Taraba tun lokacin da gwamnati ta kirkiro shirin taimakawa talakawa na kasa
Ministar Jin-ƙai Sadiya Farouq ta bayyana haka a garin Jalingo babban birnin jihar, yayin da take wata tattaunawa da waɗanda suka ci moriyar shirye-shiryen ma’aikatan.
Kamar yadda BBC Hausa ta ruwaito, Ministar wadda shugabar shirin a jihar Beatrice Kitchina ta wakilta ta ce mutum sama da miliyan 100 sun fita daga cikin kangin matsanancin talauci dalilin wannan shiri, kuma ciki har da matasa da mata a fadin kasar nan.
Ta bayyana jerin wasu shirye-shirye kamar su N-Power da CCT da GEEP ga kuma shirin ciyar da ‘yan makaranta shi ma a matsayin wasu shirye shirye da talakawa ke cin moriyarsu har yanzu a faɗin kasar nan
Sakataren shirin ciyar da ‘yan makarantar Idris Goje, yace an yi maganin talauci a ƙasa da wannan shiri, haka kuma shirin ya yi amfani matuka a jihar Taraba.