Dan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Zamfara, Dauda Lawal, ya yi zargin cewa sufeto Janar din ‘yan sandan Najeriya, Alkali Baba, ya tura tawagar jami’an tsaro na musamman domin yin magudin zabe a jihar.
Lawal, a wata sanarwa da ofishin yada labaran sa ya fitar a ranar Litinin a Gusau, ya zargi Sufeto Janar din da hada baki da Gwamna Bello Matawalle don yin magudin zaben gwamna da aka yi a jihar.
Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi 12 daga cikin 14 na jihar.
Dan takarar na PDP ne ke kan gaba bayan da ya lashe kananan hukumomi tara daga cikin 12 da aka tattara. Gwamna Matawalle na jam’iyyar APC ya lashe kananan hukumomi uku da suka rage.
“Babban abin da ke damun mu shi ne tsoma bakin babban sufeto Janar na ‘yan sanda, Usman Alkali Baba,” ofishin Lawal ya yi zargin cewa, “Mun yi kira a ranar zabe cewa babu ‘yan sanda a fadin jihar. Makirci ne da kwamishinan ‘yan sandan jihar Zamfara ya yi na taimaka wa jam’iyyar APC mai mulki wajen yin magudin zabe.”
“Majiyoyin mu da aka tabbatar sun tabbatar mana da cewa Sufeto Janar na ‘yan sandan kasar ya tura tawagar dakaru na musamman zuwa Zamfara daga Abuja aka dauke su zuwa Sokoto. Mun samu labari cewa suna kan hanyar su ta zuwa Zamfara ne domin tayar da tarzoma tare da haifar da tashin hankali a babban birnin jihar.
“Kwamishinan Zabe na Jihar Zamfara (REC) da gangar yake jinkirta bayyana sakamakon zaben, wanda hakan ya baiwa gwamna Matawalle damar shirya yin magudi.
“Duk sakamakon da aka tattara daga kananan hukumomi 14 na nan tsaf, Ba mu san dalilin da yasa suke jinkirta bayyana su ba.
Sanarwar ta kara da cewa, “Shugaban kasa, hukumomin tsaro, da masu sa ido na kasa da kasa su mai da hankali sosai kan yadda ake gudanar da bayyana sakamakon zabe a jihar Zamfara.”
Discussion about this post