Hedikwatar Tsaro ta Sojojin Najeriya ta bayyana cewa a cikin makonni biyu zaratan ‘Operation Delta Safe’ sun dagargaje ƙananan matatun fetur har 74, waɗanda mallakar ɓarayin fetur ne.
Kakakin Hedikwatar Tsaro Manjo Janar Musa Ɗanmadami ne ya bayyana haka, a lokacin da ya ke wa taron manema labarai jawabi a ranar Alhamis, a Abuja.
Ɗan masani ya ce sojojin sun lalata rinɗima-rinɗiman tankunan ɓoye mai har 341, su ka tarwatsa ƙananan kwale-kwalen lodi da jigilar mai na sata, kuma su ka lalata manyan murahun tace ɗanyen mai, da ramukan tara kayayyaki. Murahun da aka dagargaza sun kai 260.
Ɗan masani ya ci gaba da cewa an sami litar ɗanyen mai na sata har lita 209,000, sai lita 145,000 ta gas da kuma lita 4,500 ta fetur.
Haka kuma ya ce an samu makamai iri daban-daban har 27 a hannun ɓarayin mai ɗin, sai albarusai 468, jirgin ruwa mai gudun tsiya guda biyu, motoci takwas da babura huɗu.
Sannan ya ce a cikin makonnin biyu sojoji sun damƙe maɓarnata har 71.
A yankin Kudu maso Gabas ma sojoji sun ce su na ci gaba da samun galaba kan tsagerun ‘yan IPOB/ESN.
Rundunar Sojojin Najeriya sun dagargaje ƙananan matatun mai 74, mallakar gaggan ɓarayin fetur.