Hukumar Bada Lamuni ta Duniya, IMF, ta bayyana cewa Shirin Lamunin CBN ga Manoma, wato ‘Anchor Borrowers Program’, ABP, ko kaɗan bai bunƙasa fannin noma ba, saboda ba a bayar da lamunin ga ainihin manoma na gaskiya waɗanda ya kamata a bai wa lamunin ba.
IMF ya ce saboda waɗansu ne can daban aka bai wa lamunin, ba manoma gangariya ba, shi ya sa har yanzu sun ƙi biyan basukan, sai kashi 25% bisa 100% na waɗanda waɗanda suka karɓi lamunin su ka biya.
Cikin watan Nuwamba, 2015 ne Shugaba Muhammadu Buhari ya ƙirƙiro Shirin Bayar da Lamuni Ga Ƙananan Manoma, a ƙarƙashin Babban Bankin Najeriya (CBN), da nufin bunƙasa harkokin noma a hannun ƙananan manoma.
A ƙarƙashin tsarin dai CBN ta riƙa bayar da lamunin noma bisa sharaɗin cewa Duk kayan gonar da su ka noma, za su kwasa su kai wa jami’an ABP su saya, a yi ciniki su ɗebe wa gwamnati kuɗaɗen da ta ramta masu.
An umarci ƙananan manoma su riƙa noma shinkafa, masara, alkama, auduga, rogo, doya, rake, ‘ya’yan itace, tumatir da kuma kiwon dabbobi, tsuntsaye da kifi.
An riƙa bada lamunin a ƙarƙashin wasu ƙananan bankunan tallafa wa masu ƙananan masana’antu, wato ‘Microfinance Banks’, wato MDBs.
Sai dai kuma IMF tmya bayyana cewa a binciken sa, waɗanda ya kamata a riƙa bai wa lamunin kuɗaɗen ba su aka riƙa bai wa ba.
Bankin ya ce shi ya sa shirin duk da ya hana shigo da wasu kayan abinci daga waje, bai kawo sauƙi ga abincin da ake nomawa a cikin gida ba, sai ma tsawwalawa da farashin kayan abinci ke ci gaba da yi, a duk wata ko ƙasa da haka.
Ya ce kashi 24 bisa 100 kaɗai su ka biya lamunin.
Wani rahoto da PREMIUM TIMES Hausa ta taɓa bugawa a baya, an gano yadda wasu da dama su ka riƙa ƙara aure da kuɗaɗen lamunin, wasu kuma sun riƙa kwasar kuɗaɗen su na zuwa aikin Hajji ko Umra.