Yayin da ya rage ƙasa da wata ɗaya a fara shirin kidayar jama’a a Najeriya, Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ba za a tambayi kowa jinsin ƙabila ko addinin sa ba.
Ministar Harkokin Kuɗaɗe ce, Zainab Ahmed ta bayyana haka, inda ta ƙara cewa, “tambayar addini ko bin ƙwalailaitar sanin ƙabilar mutum duk abu ne da zai ƙara jawo wa ƙasar nan ja-in-ja daga bangarori daban-daban.
“Babban dalilin yin ƙidayar shi ne don a san yadda gwamanti za ta riƙa gudanar da tsare-tsaren ta na ci gaban ƙasa da bunƙasa al’umma. Sai kuma a san yankunan da jama’a su ka fi ƙaranci ko yawa, ta yadda za a gane wurin da ya fi muhimmanci ko fifikon da masu zuba jari za su fi karkata a can.”
Ta ce yin ƙidaya zai sa a san takamaimen adadin yara, manya, maza da kuma mata.
Maƙasudin ƙidayar dai shi ne don a daƙile matsala da barazanar gurɓacewar yanayi ko canjin muhalli.
Shi kuwa Ƙaramin Ministan Harkokin Kuɗaɗe, Clem Agba, ya bayyana cewa Najeriya na buƙatar kashe naira biliyan 869 wajen gudanar da ayyukan ƙidayar.
Sai dai kuma ya ce duk da saura makonni uku a fara aikin, wato daga 29 ga Maris zuwa 2 ga Afrilu, har yanzu gwamnatin tarayya ba ta da isassun kuɗaɗen gudanar da aikin ƙidayar.
Ya ce za’a yi ƙidayar a dukkan ƙananan hukumomi 774 na faɗin ƙasar nan.
Ƙaramin Ministan Kasafin Kuɗaɗe da Tsare-tsare, Clem Agba, ya ce har yanzu Naira biliyan 243 gwamnati ta iya samu.
Ya ce daga cikin Naira biliyan 869 da za a kashe, a yayin aikin zaɓen za a kashe Naira biliyan 626, sauran kuma sai bayan ƙidaya za a riƙa amfani da su wajen ayyukan ƙidayar da za a riƙa gudanarwa daga nan zuwa 2025.
Rabon da a yi ƙidaya dai tun cikin 2006. Kuma ya zuwa yanzu Hukumar Ƙidaya ta Majalisar Ɗinkin Duniya (UNFPA) ta ƙiyasta adadin ‘yan Najeriya sun kai miliyan 216.
Ana kuma fargabar cewa idan yadda ake yawan haihuwa ya ci gaba a haka, to nan da 2050 yawan ‘yan Najeriya zai iya kai miliyan 400.
Discussion about this post