Rundunar ‘Yan Sandan Najeriya ta bayyana cewa ta samu nasarar damƙe masu laifi har 781 a lokacin zaɓukan 2023 a faɗin ƙasar nan.
Sufeto Janar Alƙali Usman ne ya bayyana wannan adadi a ranar Litinin lokacin da ya ke ganawa da Mataimakan Sufeto Janar-Janar da Kwamishinonin ‘Yan Sanda da sauran manyan kwamandojin ‘yan sanda na ƙasar nan a Abuja.
Ganawar dai kamar yadda Kakakin Yaɗa Labaran Hedikwatar ‘Yan Sanda, Olumuyiwa Adejobi ya sanar wa manema labarai, ya ce an yi ta ne domin a bibiyi irin ayyukan da ‘yan sanda su ka yi a lokacin zaɓen 2023.
Usman ya umarci rundunonin jihohi su damƙa duk wani fayil na waɗanda aka kama da laifukan zaɓe ga sashen Kula da masu aikata laifukan zaɓe a hedikwata ta ƙasa.
Ya ce an kama masu laifi 203 a lokacin zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisar tarayya da Sanatoci. Sai kuma masu laifi 578 a lokacin zaɓen gwamnoni da na majalisar dokokin jihohi.
Daga nan ya yi kira ga Hukumar Zaɓe ta ƙasa ta gaggauta gurfanar da waɗannan masu laifi su 781 a kotu, domin a hukunta sai.
Daga nan ya jinjina wa manyan jami’an ‘yan sanda saboda muhimmiyar rawar da su ka taka a lokacin zaɓen 2023, musamman juriya, sadaukarwa da kuma saurin daƙile ɗaiɗaikun wuraren da aka yi hatsaniya.