Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi kira da rokon iri ga mutanen jihar Kaduna da su wa Allah su zaɓi ɗan takarar gwamna na jihar na Jam’iyyar APC, Sanata Uba Sani.
A wata sako na musamman da Buhari yayi wa mutanen jihar Kaduna ranar Laraba, shugaba Buhari ya ce ” Sabata Uba Sani ne ɗan takarar sa kuma zaɓen sa a zaɓen gwamna na jihar Kaduna da za ayi ranar 11 ga Maris.
” Ina mai rokon ku da ku zaɓe sanata Uba, ku zaɓi duka ƴan takarar APC. Sanata Uba jagora ne a cikin wannan tafiyar, Mun yi aiki tare da shi a majalisar Dattawa kuma ya nuna kwazo da jarumta. Lallai zai taka rawar gani InshaAllahu idan aka zaɓe shi gwamna a Jihar Kaduna.
” Ina baku hakuri game da canjin takardun kudi da aka yi, an yi shi ne don tattalin arzikin kasa ya bunkasa ba dun wasu su wahala ba.
Za a gudanar da zaben gwamnoni da ƴan majalisun jihar ranar 11 ga Maris.
Discussion about this post