Sabon rikici ya kunno kai cikin babbar jam’iyyar adawa, PDP, makonni huɗu bayan zaɓen shugaban ƙasa.
PDP ta dakatar da tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da kuma tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim.
Ba su kaɗai aka dakatar bayan Kunno kan ɓarakar ba. An kuma dakatar da wasu jiga-jigan jam’iyyar su biyu, waɗanda su ka haɗa da Dennis Ityavyar daga Jihar Benuwai da kuma Aslam Aliyu, daga Jihar Zamfara.
Haka nan kuma PDP ta miƙa sunan Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ga Kwamitin Ladabtarwa na PDP, bisa zargin su da aikata laifin yi wa jam’iyya zagon ƙasa, wato ‘anti-party’.
Cikin sanarwar da Kakakin PDP, Dele Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis a Abuja, bayan taron Kwamitin Zartaswar PDP ne aka ɗauki wannan mataki.
Sanarwar ta ce, “Kwamitin Zartaswar PDP ya yi nazarin abubuwan da ke faruwa a cikin jam’iyyar, inda ya yi amfani da Tsarin Mulkin PDP, wanda aka yi wa kwaskwarima cikin 2017, ya miƙa sunan Gwamna Samuel Ortom na Benuwai ga Kwamitin Ladabtarwa, domin a hukunta shi, saboda ya yi wa PDP zagon ƙasa.
“Kwamitin Zartaswa ya kuma amince da dakatar da waɗannan mambobi da su ka haɗa da:
1. Ayo Fayose, Tsohon Gwamnan Jihar Ekiti.
2. Sanata Anyim Pius Anyim, Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, daga Jihar Ebonyi.
3. Farfesa Dennis Ityavyar daga Jihar Benuwai.
4. Dakta Aslam Aliyu daga Jihar Zamfara.
“Jam’iyya ta yi kira ga dukkan ‘yan PDP su kasance a dunƙule wuri guda, kuma su fuskanci ƙalubalen da ya tunkaro PDP.”
Ortom wanda ɗan ɓangaren G5 ne, ya yi wa PDP ‘anti-party’ a lokacin zaɓen shugaban ƙasa.
Ortom dai ya fito ƙiriƙiri ya bayyana cewa Peter Obi yai goyi baya a zaɓen shugaban ƙasa.