Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Ibrahim Shema, ya gargaɗi Shugaban PDP, Iyorchia Ayu cewa ya gaggauta janye dakatarwar da aka yi masa, ko kuma ya fice daga PDP ɗin ɗungurugum.
Haka kuma Shema ya ce PDP ta sauya tunani, daga mafarkin da ta yi na rushe Majalisar Zartaswar PDP Reshen Jihar Katsina.
Shema ya yi waɗannan bayanai a cikin wata wasiƙa da ya aika wa Ayu a ranar 24 Ga Maris.
A ranar Alhamis ce PDP ta dakatar da wasu mambobin ta huɗu, ciki har da Shema bisa zargin su da yi wa jam’iyya zagon-ƙasa, wato ‘anti-fati’ a lokacin zaɓe.
Sauran waɗanda aka dakatar ɗin sun haɗa da Anyim Pius Anyim, Ayo Fayose, Dennis Ityavyar da Aslam Aliyu.
Sannan kuma PDP ta rushe shugabannin jam’iyya na reshen Jihar Katsina, maimakon su ta naɗa kwamitin shugabancin riƙo, waɗanda za su yi riƙon ƙwarya tsawon kwanaki 90.
PDP ta ce ta yi abin da ta yi bisa bin ƙa’idar Sashe na 29(2)(b) da Sashe na 31(2) E na Kundin Dokokin PDP na 2017.
PDPin Jihar Katsina ta shiga rikici tun cikin Mayu, 2022 lokacin da ta yi zaɓen fidda gwani ta fito da Yakubu Lado matsayin ɗan takarar gwamna.
Shema da wasu jiga-jigan PDP sun ƙi yarda da takarar Lado, har ma su ka ƙi halartar kamfen ɗin da Atiku ya je a Katsina cikin Disamba.
Cikin watan Fabrairu kuma gwamnatin Jihar Katsina ta janye ƙarar zargin karkatar da naira biliyan 11 da ta ke yi wa Shema.
Mutane da dama na ganin cewa saɓanin da aka samu na rarrabuwar kawuna tsakanin PDP a Katsina ya haifar da faɗuwar ta zaɓen gwamnan jihar.
Dikko Raɗɗa na APC ya samu ƙuri’u 859,892, shi kuma Lado na PDP ya samu 486,620.
Shema dai ya bai wa Ayu sa’o’i 48 ya janye rushe shugabannin PDP na da ya yi, kuma ya janye dakatarwar da ya yi masa.