Tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Anyim Pius Anyim, ya maida kakkausan raddi dangane da dakatarwar da uwar jam’iyyar PDP ta yi masu.
A makon juya ne PDP ta dakatar da Anyim, tsohon Gwamnan Ekiti Ayo Fayose, tsohon Gwamnan Katsina, Ibrahim Shema da wasu.
Yayin da tuni Shema ya yi barazanar ficewa daga PDP idan ba a janye dakatarwar da aka yi masa ba, shi kuwa Anyim ya bayyana cewa ya na alfahari da ‘anti-party’ ɗin da ya yi wa PDP, a zaɓen gwamnan Jihar Ebonyi, wanda aka yi ranar 18 Ga Maris.
Anyim dai ya ƙi goyon bayan ɗan takarar PDP, maimakon haka, ya goyi bayan ɗan takarar APC, kuma shi ɗin ne ya lashe zaɓen.
Anyim ya bayyana cewa ya ƙi goyon bayan ɗan takarar PDP ne saboda uwar jam’iyyya ta ƙasa ta ƙaƙaba ɗan takarar gwamnan da ba shi ya kamata PDP ta tsayar ba.
Ya ce a bisa tsarin adalci bai kamata ɗan takarar PDP ya fito a shiyyar ɗan takarar ba.
Ya ce akwai yankin da ɗan takarar PDP ya kamata ya fito, kowa ya san wannan, saboda yankin ma ya na da haƙƙi.
“A lokacin da Atiku Abubakar ya zo Ebonyi yaƙin neman zaɓe, na samu Shugaban PDP, Iyorchia Ayu, na ce masa ni da mutane na ba za mu halarci kamfen ɗin Atiku ba, saboda kun ƙaƙaba mana ɗan takarar gwamnan da ba shi mu ke so ba.
“Amma Ayu ya yi banza da ni, bai yi komai a kai ba. Saboda ya raina ni, don kawai ya na shugaban jam’iyya. Wannan ne dalilin da ya sa ban halarci wurin kamfen ɗin ba.
“Saboda haka da zaɓen gwamna ya zo, sai na goyi bayan ɗan takarar APC, wanda su ka tsayar takara daga yankin da mu ka so PDP ta tsayar da na ta ɗan takarar. Kuma na APC ɗin ne ya ci zaɓen gwamnan. Saboda haka ina alfahari da zagon-ƙasa ɗin da na yi wa PDP, a zaɓen gwamnan Ebonyi.”
Dangane da dakatar da shi da aka yi kuwa, Anyim ya ce raina su aka yi, kuma abin baƙin ciki ne. Ya ce bai kamata a dakatar da su ba, kamata ya yi a fara zama da su a yi ta bakin su tukunna.
Ya ce idan ma laifi ne, to shugabannin PDP ne ke da laifi, su da su ka riƙa yi wa jam’iyya abin da su ka ga dama don kawai an ba su shugabanci.
A ƙarshe ya ce akwai riƙaƙƙun ‘yan PDP waɗanda aka kasa taɓawa, kuma a kullum su na yi wa jam’iyyar da shugabannin ta shaguɓe, gugar-zana, gwasalewa, shegantaka da rashin kunya a fili.
Anyim ya ce su ya kamata a ce an dakatar idan ba tsoro Ba.
Ya ce idan aka tafi a haka, waɗannan shugabanni na PDP za su ci gaba da kawo rabuwar kawuna a cikin PDP, har jam’iyyar ta ci gaba da zaizayewa kowa ya kama gaban sa.
Discussion about this post