Ɗan takarar shugaban ƙasa na LP, Peter Obi, ya baje wa Kotun Ɗaukaka Ƙara abubuwan da ya ke buƙata da kuma dalilan sa na rashin amincewa da zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda ya zo na uku.
1. Peter Obi ya maka Bola Tinubu, Kashim Shettima da INEC ƙara.
2. A ƙarar da Obi da LP su ka shigar, sun bijiro batutuwa shida waɗanda su ke so kotu ta yi nazari, sannan ta soke nasarar da Tinubu, Shettima da APC su ka yi ta cewa su ne su ka yi nasarar zaɓen shugaban ƙasa.
3. Takarar Shettima a matsayin mataimakin Tinubu haramtacciyar ce, domin takara biyu ya fito a lokaci ɗaya, takarar Sanatan Barno ta Tsakiya, kuma ya na takarar mataimakin shugaban ƙasa.
4. Kashim Shettima bai janye takarar sa ta sanata ba kafin ya amshi takarar mataimakin shugaban ƙasa.
5. Tinubu bai cancanci takarar shugaban ƙasa ba, saboda laifin hada-hadar muggan ƙwayoyi da aka kama shi a Amurka, har hukumar ƙasar ta ƙwace dala 460,000 a hannun sa.
6. Tinubu bai cika sharuɗɗan da za’a bayyana shi zaɓaɓɓen shugaban ƙasa ba, saboda bai ci ƙuri’un da su ka wajaba ba kafin a ayyana sunan sa wanda ya yi nasara.
7. Tinubu bai samu yawan kashi 25% bisa 100 na ƙuri’un FCT Abuja ba, kamar yadda doka ta ce sai ɗan takara ya same su kafin ya yi nasara tukunna.
8. Rashin yin amfani da hanyar tattara sakamakon zaɓe da aika su BVAS da sauran hanyar na’urori kamar yadda dokar zaɓe ta tanadar.
8. INEC a cewar Obi da LP ta riƙa zabtare ƙuri’un su ta na danƙara wa wasu jam’iyyun da LP ta yi wa Pintinkau a Bayelsa, Ribas, Benuwai da wasu jihohi takwas.
9. Ƙuri’un da aka kwashe masa hakan ta hana shi yin nasara. Idan aka maida masa ƙuri’un sa, Obi ya ce shi zai yi nasara.
10. Shettima ya karɓi tayin zama ɗan takarar mataimakin shugaban ƙasa a ranar 14 Ga Yuli, a lokacin kuma bai sauka daga takarar sanatan Barno ta Tsakiya ba.
11. Dokar Zaɓe ta haramta a tsaida mutum ɗaya takarar wurare biyu a lokaci guda.
12. Jihohi 11 ne Peter Obi ya ke iƙirarin an danne masa haƙƙin NASARAR da ya yi, amma aka kwashe ƙuri’un sa, aka gabza wa wasu jam’iyyu.
13. Obi na so a soke nasarar da INEC ta ce Tinubu da Shettima sun yi.
14. Obi na so a haramta takarar Tinubu da Shettima.
15. Obi ya na so a maida masa ƙuri’un sa ya yi zargin INEC ta gabza wa wasu jami’iyyu.
16. Obi na so a ayyana shi cewa shi ne ya yi nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa na 25 ga Fabrairu, 2023.
17. Obi na so kotu ta bayar da umarni a sake zaɓen shugaban ƙasa, idan har ba ta ayyana cewa shi ne ya yi nasara ba.
Discussion about this post