Jam’iyyar APC ta yi barazanar datse hanyar shiga Hedikwatar INEC da ke Jihar Ribas a Fatakwal, idan hukumar zaɓen ta hana ta kayayyakin zaɓen da za ta yi nazari har ranar cikar wa’adi ta wuce.
APC dai ta bai wa INEC wa’adin sa’o’i 72 cewa ta umarci ofishin ta na Jihar Ribas ya damƙa wa jam’iyyar bayanan da ta ke nema domin kafa hujja da su a ƙarar da ta shigar Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓe.
INEC dai ta bayyana sunayen Sanatoci uku na PDP da ‘yan majalisar tarayya 9 na daga cikin 12 duk na PDP cewa su ne su ka yi nasara a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu, 2023 a Jihar Ribas.
Sai dai kuma ganin cewa APC ta yi nasarar ɗan majalisar tarayya ɗaya tilo, ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙarar Zaɓe, ta kai ƙara cewa, “an yi wa ‘yan takarar ta fashi da satar sakamakon zaɓe, domin su ne su ka yi nasara.”
Daga nan APC ta yi barazanar yin zanga-zangar da za su tare hanyar shiga ofishin INEC na Fatakwal, idan har wa’adin sa’o’i 72 su ka cika INEC ba ta ba su abinda su ke buƙata ba.
A wani rincimin tun cikin makon da ya gabata kuwa, Kotu ta bai wa INEC iznin yi wa na’urorin BVAS garambawul.
Babbar Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta bai wa INEC iznin yi wa na’urar tantance masu katin shaidar zaɓe garambawul ɗin loda masu ƙaidojin aikin zaɓen gwamnoni da na majalisar jihohi.
Kotun ta amince su yi wa na’urorin waɗanda aka yi aikin zaɓen shugaban ƙasa da na Majalisun Tarayya da na Dattawa, bayan kuma ta bai wa Atiku, Obi da Tinubu iznin su binciki BVAS ɗin.
Wannan jarida dai ta buga labarin INEC ta nemi kotu iznin yi wa na’urorin BVAS garambawul kafin zaɓen gwamnoni.
Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC), ta garzaya Kotun Ɗauka Ƙara domin neman iznin yi wa na’urorin tantance masu rajistar zaɓe (BVAS) garambawul, kafin zaɓen ranar 11 ga Maris.
Za a yi zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki jihohi a ranar Asabar, 11 ga Maris.
INEC ta garzaya kotun ne kwana biyu bayan kotu ta bai wa Atiku Abubakar na PDP da Peter Obi na LP iznin binciken na’urorin BVAS waɗanda aka yi zaɓen shugaban ƙasa da na majalisar tarayya da su.
Sun nemi iznin ne domin su ƙara kafa wa kotun hujjojin da su ke dogaro da su dangane da zargin maguɗin da su ke cewa an yi a zaɓen ranar 25 ga Fabrairu.
Sai dai kuma INEC ta je Kotun Ɗaukaka Ƙara ta na neman a ɗage mata hukuncin hana ta taɓa na’urorin BVAS bayan zaɓen shugaban ƙasa.
Kotun ta hana INEC taɓa su ne, saboda ta bai wa PDP da LP iznin binciken na’urorin domin su gano zargin maguɗin da su ke iƙirarin an yi, idan har an yi ɗin.
Sai dai kuma kwanaki biyu bayan an bai wa su Atiku iznin binciken BVAS, ita ma INEC ta garzaya Kotun Ɗaukaka Ƙara ta nemi iznin cewa a ba ta damar yi wa na’urorin garambawul saboda da su ne za ta yi aikin tantance masu zaɓen ranar 11 ga Maris.
INEC ta ce idan ba ta yi masu garambawul ɗin ba da wuri saboda an ce ta nesance su, tunda an bai wa Atiku da Obi iznin binciken su, to sai dai fa idan ɗage zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki za ta yi.
Ta kafa hujjar cewa ba a Abuja ake aikin yi wa na’urorin garambawul ba, kuma aikin ya na ɗaukar lokaci.