Mashawarcin Musamman a Harkokin Yaɗa Labaran Rundunar Yaƙin Neman Zaɓen Bola Tinubu, mai suna Dele Alake, ya ce ba fa lallai tilas ba ne sai INEC ta watsa sakamako ko ta tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ta hanyar amfani da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe, wato BVAS.
Alake ya yi wannan bayani a ranar Juma’a a Abuja wurin taron manema labarai.
Ya ce INEC ce kawai ta ke da wannan hurumin, idan ta ga dama ta yi, idan kuma ba ta ga dama ba, ba lallai ba ne sai ta yi haka ɗin.
Alake ya ce Dokar Zaɓe ta 2022 ba ta tilasta wa INEC yin hakan ba.
“Masu ƙorafin INEC ba ta bi ƙaidar amfani da BVAS wajen tattara sakamakon zaɓen shugaban ƙasa ba, ba su da wata madogara wadda za su kafa a dokance.
“Saboda Sashen Dokar Zaɓe na 2022 da PDP ke ta ɓaɓatu a kan sa, ita da LP, har su ke ƙoƙarin garzayawa kotu, ba shi da wata alaƙa da batun tattara sakamakon zaɓe ta hanyar BVAS.
“Sashe na 60 a cikin ƙaramin sashe na 2 ya nuna sai idan INEC ta ga dama ta yi, idan kuma ta ga wata damar, ba lallai sai ta yi ba.
“Don haka tsarin aikawa da sakamakon zaɓe daga rumfunan zaɓe a ranar da aka yi zaɓe ko ma bayan kwana biyu da yin zaɓe ne, ba zai canja sakamakon zaɓe ba.” Inji Alake.
Halin Da Ake Ciki A Kotun Ɗaukaka Ƙara:
Kotun Ɗauka Ƙara ta bai wa Atiku da Obi iznin duba na’urorin aikin zaɓen INEC.
Kotun Ɗaukaka Ƙara ta Abuja ta bai wa ɗan takarar shugaban ƙasa Atiku Abubakar da takwaran sa Peter Obi iznin binciken na’urorin da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi amfani da su wajen gudanar da zaɓen shugaban ƙasa a 2023.
Atiku na PDP da Obi na LP sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na da Majalisar Dattawa da ta Tarayya.
Su biyun dai Bola Tinubu ne na APC INEC ta bayyana cewa ya yi nasara a kan su.
Su biyun dai kowa ya shigar da ta sa ƙarar daban-daban, wadda su ka ce INEC ba ta bi doka wajen tattara sakamakon zaɓe ba.
Ɓangarorin biyu sun nemi kotu ta ba su iznin binciken na’urorin da INEC ta yi amfani da su wajen zaɓe.
Sun ce binciken na’urorin zai taimaka masu wajen yi wa kotu bayanin irin ƙarar da za su shigar da kuma ƙara bijiro da hujjojin da za su gabatar wa kotu.
Idan za a iya tunawa, tun kafin a kai ga bayyana sakamakon zaɓe shi ma tsohon Shugaban Ƙasa, Olusegun Obasanjo ya ce akwai harƙalla a zaɓen shugaban ƙasa, amma a kai zuciya nesa.
Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo ya yi zargin cewa an cukurkuɗa sakamakon zaɓen shugaban ƙasa.
Obasanjo ya yi kira ga Shugaba Muhammadu Buhari ya sa sake bibiyar gaba ɗayan yadda aka tattara sakamakon zaɓen.
Haka Obasanjo ya bayyana a cikin wata wasiƙar da shi da kan sa ya sa wa hannu a ranar Litinin.
Ya yi zargin cewa “yawancin sakamakon zaben da aka tattara ba tare da na’urar tantance masu katin shaidar rajistar zaɓe (BVAS da Manhajar Tattara Sakamakon Zaɓe (Server) ba, ba su nuna haƙiƙanin gaskiyar abin da ‘yan Najeriya su ka zaɓa ba.”
Obasanjo dai na ɗaya daga cikin masu goyon bayan jam’iyyar LP, wadda Peter Obi ne ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar.