Ɗan takarar Sanatan Abiya ta Arewa na PDP, M.A.O Ohuabunwa, ya ce bai amince da nasarar da INEC ta bayyana Uzor Kalu na APC ya yi a kan sa ba.
Ohuabunwa ya shaida wa manema labarai a Umuahia cewa INEC ta karya Dokar Zaɓe yayin da ta bayyana sakamakon zaɓe, bayan kuma ta rigaya ta ce “zaɓen bai kammalu ba.”
Ya ce a ranar Lahadi INEC ta shirya za ta sake zaɓen rumfunan zaɓe wajen 100 a ƙaramar hukumar Arochukwu, Ohafia da wata ƙaramar hukuma, amma kuma sai ta ɗaga zuwa Litinin.
“Mun tattara mutanen mu su ka yi tururuwar zuwa jefa ƙuri’a, sai INEC kawai ji mu ka yi INEC ta yi sanarwar wanda ya yi nasara, alhali hukumar na sane da cewa ba a kammala zaɓen ba ma.
Saboda haka ba mu yarda ba, a soke zaɓen kawai a sake wani sabo daban a rumfunan guda 100.
“Akwai rumfuna sama da 100 masu aƙalla mutum 60,000, kuma a yankin mazaɓa ta su ke ” inji Ohuabunwa.
“Ni ban damu da wanda duk ya yi nasara ba. Abin da kawai na ke so shi ne a yi sahihin zaɓe bisa gaskiya da adalci.”
INEC ta bayyana Kalu ya yi nasara da ƙuri’u 30,805. Nnamdi Iroh na LP kuma 27,540. Sai Ohuabunwa na PDP mai 15,175.
[3/2, 12:48 PM] AMB: Idan za a tuna, Kalu ya so fitowa takarar zaɓen shugaban ƙasa idan da an bi tsarin karɓa-karɓa an bar wa yankin ƙabilar Igbo su fito da ɗan takarar su a APC.
Rashin yin hakan ne a lokacin Kalu ya yi tir da ‘yan takara daga Kudu-maso-yamma da na Kudu-maso-kudu, ya ce zai janye tunda ba su ganin mutuncin ƙabilar Igbo.
Mun buga labari a lokacin wanda Bulalar Majalisar Dattawa, Sanata Orji Kalu wanda ke neman fitowa takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin APC, ya yi tir da duk wani ɗan takarar shugaban ƙasa da ya fito daga Kudu-maso-yamma da na Kudu-maso-kudu.
Ya ce tunda ba su ganin daraja da mutuncin yankin Kudu-maso-gabas, ballantana har su yi adalci su bar wa yankin takarar shugaban ƙasa, to shi zai janye daga shiga takarar.
Haka Kalu ya bayyana a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Talata.
Kalu bai ware ɗan takarar APC ko PDP ba, ya ce kamata ya yi su mutunta haƙƙin zamantakewa duk su janye su bar wa ɗan ƙabilar Igbo ya fito takarar shugabancin ƙasar nan.
Idan ba a manta ba, a farkon wannan watan ne Kalu ya ce zai fito takara a ƙarƙashin APC, idan har aka bar wa ‘yan ƙabilar Igbo su yi shugabancin Najeriya cikin 2023.
Ya zargi ‘yan takarar da su ka fito daga kudu da yi wa ƙabilar Igbo rashin adalci.
Kalu ya daɗe ya na kakabin neman a yi adalci a bar ‘yan ƙabilar Igbo su yi takarar shugabancin ƙasa a 2023 a tsakanin su.
Kalu ya ce duk da ya na son tsayawa takarar shugabancin Najeriya, to ba zai iya ƙaddamar da takarar sa, ba tare da goyon bayan yankin Kudu-maso-kudu da Kudu-maso-yamma ba.
Saboda haka ne ya ce ba shi da zaɓi, sai dai ya “koma Majalisar Dattawa, ya nesanta kan sa daga zaɓen shugaban ƙasa ko takarar zaɓen.”
“Ina mamakin ganin yadda ‘yan takara suka fito birjik daga Kudu-maso-yamma da Kudu-maso-kudu daga ɓangare biyu, wato APC da PDP. Abin kunya ne sosai, ganin yadda ba su ko ganin kima ko mutuncin yankin Kudu-maso-gabas, wanda bai taɓa samar da shugaban ƙasa mai cikakken ikon dimokraɗiyya ba.
“Na yi tunanin za su tuna da mu su goya mana baya, ɗan Kudu-maso-gabas ya yi shugabanci a 2023. Amma idanun su sun rufe, sai bindiga suke ta yi da kuɗi. Sun manta kuɗi ba ya sayen kujerar shugaban ƙasa.”