Yanzu dai kowa ya san cewa Bola Ahmed Tinubu ne magajin kujerar da Shugaba Muhammadu Buhari zai sauka a ranar 29 Ga Mayu. Tinubu ya samu nasarar lashe zaɓe da ƙuri’u 8,784,736, inda ya yi nasara kan sauran ‘yan takara su 17.
A jawabin sa na karɓa da amincewa da sakamakon zaɓe, Tinubu ya ce “zai riƙe kowa da adalci”, kuma zai “bi turbar da ake so a kai gaci.” Sannan kuma ya yi wa masu adawa tayin su haɗa kai a gina ƙasaitacciyar Najeriya.
Shi kuwa Shugaba Buhari, a saƙon sa na taya Tinubu murnar lashe zaɓe, ya ce Tinubu ɗin ne ya fi dacewa ya shugabanci ƙasar nan bayan ya sauka.
Sai dai kuma duk da giringiɗishin murnar lashe zaɓe da ake yi, daga cikin manyan ‘yan adawa uku babu wanda ya taya Tinubu murnar lashe zaɓen. PDP da LP har ma da wasu jam”iyyun duk sun ƙi amincewa da sakamakon zaɓen, tare da cewa INEC ta yi masu maguɗi. Sun ma fice daga Cibiyar Tattara Sakamakon Zaɓe, tun lokacin da su ka fahimci INEC ta kasa loda sakamakon zaɓen a BVAS domin a gani a manhajar tattara sakamakon zaɓe, kamar yadda Dokar Zaɓe ta 2022 ta tilasta, kuma ita ma INEC ɗin ta sha nanata cewa za ta yi hakan.
Matsala ta farko da ake tankiya a kan ta, ita ce kasa yin amfani da BVAS ta loda sakamakon zaɓe na kwafen takardun da ejan-ejan su ka sa wa hannu daga rumfunan zaɓe. Sai bayan kwana ɗaya sannan INEC ta danganta kasa loda sakamakon dalilin matsalar na’urorin aiki. Hakan ma sai bayan da ta ga ƙorafe-ƙorafen jama’a da kuma ragargazar da ake yi wa INEC ta yi yawa, sannan ta fito ta yi bayanin.
Rashin bin wannan dokar da INEC ta yi kuwa ya haifar da zargin maguɗin zaɓe mai ƙarfin gaske da jam’iyyu su ka yi wa INEC. APC wadda ta yi nasara ce kaɗai ba ta soki kasa loda sakamakon ba. Ita cewa ta yi ma ai ba dole sai INEC ta loda sakamakon ba.
Kungiyoyin sa-ido su ma sun bayyana cewa an samu bambance-bambance tsakanin sakamakon zaɓen da ke hannun su da kuma wasu sakamakon da INEC ta bayyana.
An samu rahotannin fizgen akwatinan zaɓe, lalata ƙuri’un da masu zaɓe su ka rigaya su ka dangwala wa yatsun su, harbe-harben bindigogi a rumfunan zaɓe, razanar da masu zaɓe, ji wa wasu raunuka ko harbin wasu, waɗanda hakan duk hujjoji ne ƙarara.
Akwai kuma damuwa sosai dangane da yadda hususan aka gudanar da zaɓen. A kan haka ne Buhari ya ce wa sauran ‘yan takara duk mai hujjar cewa an yi harƙalla a zaɓen to ya garzaya kotu. A kan haka ne PREMIUM TIMES ta ƙara jaddada matsayin ta na cewa tilas a dimokraɗiyya sai an yi aiki da doka da kundin tsarin mulki.
A sani, babu mai haddasa da nasarar da Tinubu ya samu idan aka yi la’akari da ƙalubalen da ake magana an fuskanta.
Maganar da Tinubu ya yi cewa zai yi adalci kuma zai yi abin da ‘yan Najeriya ke so a yi don a kai gaci, wannan kuma wani ƙalubale ne da ya rataya wa wuyan sa. Saboda ba za mu manta ba, a ranar da aka rantsar da Shugaba Buhari, ya ce, “Ni na kowa ne, amma kuma ba zan nuna sani ko sabo a kan wasu ba.” Amma maganar gaskiya bai cika wannan alƙawarin ba.
Ya riƙa nuna ɓangaranci, shiyyanci da kusanci wajen bayar da manyan muƙamai, lamarin da ya haifar da gwamnatin sa ta koma kamar mahaucin da ba shi da wuƙa mai kaifi, sai dakusassa. Irin yadda Tinubu zai kafa gwamnatin sa ne zai sa a gane wace irin Fadar Shugaban Ƙasa zai gina mulkin sa da ita.
Najeriya ta ko’ina a ruguje ta ke, ta na buƙatar haziƙan da za su sake gina ta. Kare rayuka da dukiyoyin jama’a shi ne maƙasudin kafa gwamnati.
Musamman a Arewa yanzu ran mutum ba a bakin komai ya ke ba, saboda mahara ‘yan bindiga masu garkuwa da mutane. Ga kuma Boko Haram.
Makarantu da dama a Arewa duk a rufe su ke saboda fitinar ‘yan bindiga. Yayin da ake kashe rayukan jama’a kamar kiyashi, kashe-kashen bai tsallake sojoji da ‘yan sanda ba.
Akwai jan aiki sosai wajen daƙile rashawa da cin hanci a ƙasar nan, yaƙi da cin hancin da ake yi kai ka ce takin zamani ne ake ƙara baɗawa kan shuka. Satar biliyoyin kuɗi da manyan ma’aikata da shugabannin siyasa ke yi ya sa an daina ganin darajar gwamnati. Jama’a kawai na yi mata kallon wani babban kamdamin da ake shiga don a saci maƙudan kuɗaɗe, amma ba don kishin ƙasa da al’ummar ta ba.
Matsalar tattalin arziki, tsadar rayuwa, matsalar rashin wutar lantarki da matsalar tsaro sun kashe kasuwanci da masana’antu da dama.
Zaɓaɓɓen Shugaban Ƙasa zai gaji kasafin kuɗi mai giɓin naira tiriliyan 11.34. Abin takaici maƙudan kuɗaɗen al’umma na hannun manyan ɓarayin gwamnati su na bushasha duniya na kallo.
Wani abin takaicin kuma akwai kuɗaɗen Najeriya har dala biliyan 62 a hannun kamfanonin mai, an kasa karɓowa tun cikin 2018. Sai ga shi abin mamaki kuma NNPCL ta ce a kowane wata Najeriya na kashe naira biliyan 400 wajen biyan tallafin fetur.
Babban aikin Tinubu kuma akwai batun tsaftace fannin fetur domin ko mahaukaci ya san maƙudan kuɗaɗen da ake asara a fannin ɗanyen mai, idan gobace ai jami’an kashe gobara ba za su bari ta yi irin wannan muni haka ba.