Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC), ta bayyana Dr Dikko Umar-Radda na jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Katsina da aka gudanar a ranar 18 ga watan Maris.
Da yake bayyana sakamakon zaben a ranar Lahadi a Katsina, jami’in zaɓen gwamnan jihar, Farfesa Muazu Abubakar-Gusau, mataimakin shugaban jami’ar tarayya da ke Gusau, ya ce Umar-Radda ya samu kuri’u 859,892 wanda ya zama zababben gwamnan jihar.
Ya ce Umar-Radda ya doke abokin takarar sa Sen. Yakubu Lado-Danmarke na jam’iyyar PDP wanda ya samu kuri’u 486,620.
Abubakar-Gusau ya kara da cewa ‘yan takara daga jam’iyyu 13 ne suka fafata a zaben.
Abubakar-Gusau ya kara da cewa ‘yan takara daga jam’iyyu 13 ne suka fafata a zaben.
Ya ce adadin wadanda suka yi rajistar zabe a jihar ya kai 3,516,719, yayin da adadin wadanda suka kaɗa zaben ya kai 1,399,291.
Ya kara da cewa adadin kuri’un da suka lalace sun kai 20,575.
Discussion about this post