Reshen PDP na Jihar Ribas ya yi zargin cewa APC, LP da SDP sun shirya dasa bama-bamai a ofisoshin INEC na jihar.
“Mun ji labarin tsiyar da wasu jam’iyyu ke ƙullawa, cikin su har da APC, LP da SDP, su na shirin dasa bama-bamai a ofisoshin INEC na cikin yankunan karkara.”
Daraktan Yaɗa Labaran PDP Reshen Jihar Ribas, Ogbonna Nwuke ne ya bayyana haka, a cikin wata sanarwar da a fitar kuma ya raba har zuwa ga PREMIUM TIMES.
Nwuke dai bai bayar da cikakken bayanin irin ‘tsiyar’ da ya ce ake ƙullawa ba, amma dai “su na shirin dasa bama-bamai domin su karkashe ma’aikatan zaɓe, waɗanda babu ruwan su da siyasa. Za su yi haka ne don su tarwatsa zaɓe, kuma su hargitsa cibiyoyin tattara sakamakon zabe.”
Jami’in na PDP ya yi wannan iƙirarin yayin da ya ke magana dangane da wani zargin cewa wasu gwamnonin PDP biyar na ta ƙoƙarin haɗa baki da wasu ɓatagarin jami’an zaɓe domin su yi maguɗin zaɓen gwamnoni da na majalisar dokoki, wanda za a yi a ranar Asabar mai zuwa.
Zargin dai Tonye Cole ne, ɗan takarar gwamnan APC na jihar Ribas ya yi shi.
Nwuke ya ce wannan magana ta Cole shirme ce da kuma faffakar wofi, irin wadda gigitattu ke yi har ta kai su na kai wa iska naushi saboda wawanci._
Ya ƙara da cewa jam’iyyun da ke zargin wai PDP na shiri tare da INEC domin ta yi maguɗin zaɓen gwamnan Ribas, shirmen na su ya yi kama da manomin da ya raina ruwan farko ya ƙi yin shuka, saura su ka yi, kuma aka bar shi a baya, saboda bai yi shuka ba.