Jam’iyyar PDP ta sanar da janye dakatarwar da ta yi wa tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, Anyim Pius Anyim, tsohon Gwamnan Jihar Katsina,, Ibrahim Shema, tsohon Gwamnan Jihar Ekiti, Ayo Fayose da sauran waɗanda aka dakatar.
Haka nan ta janye gayyatar da aka yi wa Gwamna Samuel Ortom na Jihar Benuwai, wanda aka nemi ya gurfanar gaban Kwamitin Ladabtarwa na PDP.
Wata sanarwa da Kakakin Yaɗa Labarai na PDP, Debo Ologunagba ya fitar a ranar Alhamis a Abuja ta na ƙunshe da cewa janye dakatarwar an yi tattaunawa sosai kan sa.
Ya ce an janye ne bayan taron ranar Alhamis, 30 Ga Maris, 2023 domin a buɗe ƙofofin sulhu, ta yadda jam’iyyar za ta ƙara ƙarfi da karsashi.
An janye dakatarwar kwana biyu bayan kotu ta bai wa Shugaban Jam’iyya, Iyorchia Ayu umarnin ya sauka daga shugabancin jam’iyya, tunda an dakatar da shi daga cikin jam’iyya baki ɗaya.
PREMIUM TIMES Hausa ta buga labarin Shugaban Jam’iyya Ayu ya sauka, an naɗa Umar Damagum riƙon ƙwarya.
Rikicin PDP ya ci Shugaban Jam’iyya, Sanata Iyorchia Ayu, wata ɗaya bayan zaɓen shugaban ƙasa
Ayu ya bi umarnin Babbar Kotun Jihar Benuwai, wadda a ranar Litinin ta yanke hukuncin cewa kada ya ƙara kiran kan sa Shugaban PDP, tunda shugabannin mazaɓar ƙauyen su sun dakatar da shi.
Majalisar Zartaswar PDP (NWC) ce ta kira taron gaggawa ranar Talata, inda ta ce ta bi umarnin Babbar Kotun Benuwai wadda a ranar Litinin ta dakatar da Ayu, bayan wani ya maka shi kotu, ya ce a tilasta dakatarwar sa, kamar yadda mazaɓar sa su ka ce sun yi.
NWC ya ce ya yi amfani da Sashe na 45 (2) na PDP dokokin 2017, ta naɗa Mataimakin Shugaba na Arewa, Ambasada Umar Damagum a matsayin shugaban riƙo daga ranar Talata, 28 ga Maris, 2023.
Discussion about this post